✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kasashe 10 ne za su halarci Kasuwar Duniya ta Kaduna

Aminiya: Yaushe ne za a fara gudanar da bikin baje kolin Kasuwar Duniya ta Kaduna na bana?A yanzu mun kammala shirye-shirye tsaf don gudanar da…

Aminiya: Yaushe ne za a fara gudanar da bikin baje kolin Kasuwar Duniya ta Kaduna na bana?
A yanzu mun kammala shirye-shirye tsaf don gudanar da kasuwar baje koli karo na 37 da ke ci ko wace shekara a Kaduna. Kasuwar da aka saba ci duk shekara za ta gudana ne tsakanin ranar 26 ga watan Fabrairu zuwa 6 ga watan Maris wato tsawon kwanaki 10 ke nan. Kuma taken baje kolin na bana shi ne “Habbaka harkar ma’adinai don gina arzikin kasa”.

Aminiya: kasashen ketare nawa ne za su halarci kasuwar?
Akalla kasashe 10 sun nuna burinsu na baje koli, sannan ana sa ran wasu za su biyo baya. Sannan akwai dimbin kamfanoni da ’yan kasuwa na cikin gida da za su baje kolinsu.

Aminiya: Wace shawara kake da ita domin gwamnati da bankuna su tallafa wa ‘yan kasuwa?
Muna son bankuna su rinka tallafa wa manya da matsaikata da kuma kanana manoma domin su ciyar da kasa abinci da burin ganin an yi fiton rarar da aka samu. Yakamata gwamnati ta san cewa kasar Afirka ta Kudu tana samun amfanin gona a kadada daya fiye da yadda manomin Najeriya ke samu. Ya dace a gano matsalar domin a kara jan hankalin mutatne da yawa su koma aikin noma da kiwo gadan-gadan.

Aminiya: Me kuke yi don tallafa wa al’umma?
Muna shirya gasar kacici-kacici domin ’yan makarantar gaba-da firamare domin na baya su dage don neman ilimi. Kuma wannan shi ne shiri karo na biyar da zamu gabatar.

Aminiya: Akwai wani kalubale da kuke fuskanta?
daya daga ciki shi ne yadda bankuna ke tsawwala kudin ruwa a kan bashin ga ’yan kasuwa. Domin ana ba da ba shi da burin neman kazamr riba wato har kashi 10 zuwa sama, wanda bai dace ba. Abin da muke bukata shi ne ya zamo ba da bashi baya wuce kashi biyu bisa abin da aka kara. Misali idan mutum ya karbi naira miliyan daya, idan lokaci mayar wa ya yi, sai ya mayar da riban naira dubu dari biyu. Yin haka zai habbaka jama’a su rungumi harkar kasuwanci don dagaro da kansu gadan-gadan.

Aminiya: Jama’a na damuwa da yadda ’yan kasuwa ke shigo da kayayyaki marasa inganci. Me ra’ayinka kan wannan?
Shi ya sa muke shawaratar gwamnati da ta zaburi hukumar tantance ingancin kayayyaki ta kasa wato SON da ta kara zage damtse domin ganin kaya masu inganci kadai aka bari suka shigo kasar nan. Wannan zai sa mutane su ci moriyar kudinsu. Maganini haka shi ne a tallafa wa ’yan kasa domin su rinka kera abin da ake so a Najeriya ba mu rinka dogaro da kasashen waje ba.

Aminiya: Akwai mutanen da kuka kawo wannan ziyarar tare, ko za ta bayyana mana su?
Wannan tawaga ta kunshi ni Dokta Abdul Alimi Bello da Alhaji Rasak Raji da Alhaji Gimba Ibrahim da Hajiya Farida Muhibbat Dankaka da Kanar Usman Dudu (Murabus)  da Alhaji Aminu Ashiru (Sarkin Kudan) da Alhaji Suleiman Aliyu da Alhaji Usman Saulawa da kuma Alhaji Aminu Lere.