Argentina ta koma ta daya a kan jadawalin kasashen da ke kan gaba ta fuskar kwarewa wajen taka leda a duniya kamar yadda FIFA ta sanar.
Karon farko da Argentina ta hau kan wannan matakin tun bayan shekara shida, wadda ta lashe Kofin Duniya a Qatar a 2022.
- NAHCON ta sanya N2.8m a matsayin kudin kujerar Hajjin 2023
- Kwamitin Abba Gida-gida ya gargadi kananan hukumomi kan almubazzaranci
Argentina ta samu wannan ci gaban bayan nasara biyu a wasan sada zumunta da ta ci Panama da Curacao, yayin da ita kuwa Brazil rashin nasara ta yi a hannun Morocco.
Faransa, wadda ta doke Netherlands da Jamhuriyar Ireland a wasannin neman shiga Euro 2024 ta koma ta biyu.
Brazil wadda take matakin farko ta koma ta uku, Ingila wadda ta ci Italiya da Ukraine tana ta biyar da Sifaniya a jerin ’yan 10 farko.
Jerin goman farko a Fifa
1 Argentina
2 France
3 Brazil
4 Belgium
5 England
6 Netherlands
7 Croatia
8 Italy
9 Portugal
10 Spain
Super Eagles wadda Jose Pesseiro ke jan ragama ta yi kasa a jadawalin tawagogin da ke kan gaba a taka leda a duniya.
Najeriya wadda ta je ta ci Guinea Bissau 1-0 a watan jiya a wasan cikin rukuni a neman shiga kofin Afirka tana ta 40 a duniya, wadda take ta 35 a Disamba.
A nahiyar Afirka kuwa Super Eagles wadda take ta biyar a baya yanzu Masar ta karbi gurbin, Najeriya ta yi kasa zuwa ta shida.
Itama Kamaru ta yi kasa daga mataki na hudu a baya yanzu tana ta bakwai a Afirka.
Jerin 10 farko a tamaula a Afirka
1 Morocco
2 Senegal
3 Tunisia
4 Algeria
5 Masar
6 Najeriya
7 Kamaru
8 Ivory Coast
9 Burkina Faso
10 Mali