Majalisar Dinkin Duniya ta amince da sauya sunan kasar Jamhuriyar Turkiyya a kundinta daga Turkey zuwa “Türkiye”, biyo bayan bukatar hakan da aka gabatar mata.
Kakakin Majalisar, Stephane Dujarric, ya ce sun karbi wasika a ranar Laraba daga Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu, zuwa ga Babban Magatakardar Majalisar, Antonio Guterres kan bukatar sauya sunan kasar zuwa “Türkiye”.
Jami’ar Jos za ta binciki masu gadin ta kan zargin muzguna wa dalibanta
Kakakin ya ce sauyin sunan ya soma aiki ne daga lokacin da majalisar ta samu wasikar.
A ranar Talata Cavusoglu ya ba da sanarwar mika wasikar a hukumance ga Majalisar da sauran kungiyoyin kasa da kasa.
Wasikar ta ce, “Mu da daraktocinmu na sadarwa mun yi wa batun kyakkyawan shiri. Mun nuna wa Majalisar da sauran kungiyoyin kasa da kasa tabbatar wannan sauyin.”
Tun a watan Disamban da ya gabata Turkiyya ta soma yunkurin sauya sunan nata a hukumance bayan da Shugaban Kasar, Recep Tayyip Erdogan ya bukaci al’ummar kasar su koma kiran kasar da sunan ‘Türkiye’
“An yarda a rika kiran kasar da sunan Türkiye a ciki da wajenta,” inji Erdogan.
Turkiyya dai ta ce sabon sunan ya fi dacewa da al’adu da tarihin mutanen kasar, tare da umartar kasahen duniya su koma kiranta da shi.