✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasar Mali ta yi sabon fira minista

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali, Bah N’Daw ya nada jami’in huldar diflomasiyyar kasar mafi dadewa, Moctar Ouane a matsayin sabon Fira Minista. Matakin dai…

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali, Bah N’Daw ya nada jami’in huldar diflomasiyyar kasar mafi dadewa, Moctar Ouane a matsayin sabon Fira Minista.

Matakin dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan sojojin da suka jagoranci juyin mulki a kasar suka damka ragama ga Mista Bah, wanda tsohon soja ne a matsayin wani bangare na yinkurin da ake yi  na ganin makwabtan kasar na Afika ta yamma sun cire takunkumin da suka kakaba mata saboda juyin mulkin.

A watan da ya gabata ne dai sojojin suka jagoranci hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

Moctar, mai kimanin shekaru 64 dai ya taba zama ministan harkokin wajen kasar daga shekarun 2004 zuwa 2011.

Tun lokacin ne yake zama wakilin kasar ta Mali a Hukumar Kula da Tattalin Arziki ta Kungiyar ECOWAS.

Sabon shugabancin Malin dai na da gagarumin kalubalen shirya zabe cikin watannin 18 masu zuwa tare da mika ragamar kasar ga zababbiyar gwamnati kamar yadda kasashen na ECOWAS suka bukata.

Kasashen guda 15 sun dauki matakan ne ciki har da na kulle kan iyakokinsu da kasar domin dakatar da duk wata hanya da kudade za su shigo mata.

To sai dai yanzu da abubuwa suka fara daidaita ana sa ran kasashen za su janye takunkuman da suka sanya mata.