Wadansu mutum biyar sun gamu da hadarin ruftawar kasa a kansu a kauyen Baruma da ke karamar Hukumar babura da ke Jihar Jigawa inda biyu daga cikinsu suka rasu nan take.
Mutum biyu sun rasu ne sakamakon danne su da kasar ta yi a wurin hakar kasa yayin da sauran mutum uku kuma suke kwance a Babban Asibitin babura likitoci na kokarin ceton rayukansu
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce hadarin ya faru ne da misalin karfe daya da minti arba’in na ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da Mati A. Bako dan shekara 17 da Aminu Kwalle dan shekara 25 da kuma Sanka Haruna dan shekara 31 da Aliyu Yusuf mai shekara 20 dukansu mutanen kauyen Baruma, kuma Mati A. Bako da Aminu Kwalle ne suka rasu.
Ya ce bayan likita ya tabbatar da rasuwarsu an mika gawarwakinsu ga iyalansu inda aka yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.