✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Kasa da likitoci 40,000 ne suke duba ’yan Najeriya miliyan 200’

A Najeriya dai kowanne likita kan duba kusan mutum 4,000.

Shugaban Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) Farfesa Innocent Ujah ya ce kasa da likitoci 40,000 ne suke duba ’yan Najeriya sama da miliyan 200.

Ya ta’allaka matsalar a kan  yadda a kullum likitocin ke tururuwar barin kasar zuwa ketare domin neman sauyin rayuwa.

Ya ce la’akari da shawarar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayar, kamata ya yi likita daya ya rika duba mutum 600, amma a Najeriya kowanne likita kan duba kusan mutum 4,000, wani wajen ma har sama da haka.

A wasu Jihohin kamar Kano misali, gwamnati kan kashe miliyoyin kudade wajen tura su karo karatu, amma da zarar sun kammala shekarun yarjejeniyarsu ta aiki sai su cika wandunansu da iska.

A Asibitin Koyarwa na Maalam Aminu Kano da ke Jihar Kano alal misali, Dokta Fatima Damagun, wata likita ta ce a cikin shekara uku, sama da likitoci 20 ne suka bar asibitin suka tafi kasashen ketare, yayin da wasu kuma da dama ke da niyyar yin hakan.

Daga cikin wadanda suka tafi a kwanan nan a cewarta, wanda ya fi basu takaici shi ne na wasu mutum biyu; ciki har da wani Farfesa a bangaren Laka wanda shi ma ya gudu ketaren.

“Kasar Saudiyya alal misali tana dibar likitoci masu yawa a kwanan nan, kuma musamman wadanda suka fito daga Arewacin Najeirya, yayin da wadanda suka fito daga Kudanci suka fi sha’awar zuwa kasar Amurka,” inji Dokta Fatima.

A cewarta, daga tattaunawarta da yawancin abokan aikinta, muhimman dalilan da ke sa su fita sune karancin yanayin aiki mai kyau da kuma karancin kudade.

Ta ce hatta Farfesan Lakar da ya fita ya bar kasar a gidan haya ya bar iyalinsa sakamakon tsawon shekarun aikinsa bai iya gina gida ba saboda karancin kudi.

“Sai bayan ya bar Najeriya zuwa Saudiyya ne ya sami damar sayen gida sannan ya yi masa kwaskwarima yadda yake bukata,” inji ta.

Ta ce ba karamin abin kunya ba ne a wajensu a ce kullum sai sun rika tura mara sa lafiya zuwa wasu asibitocin saboda karancin ko kuma rashin kayan aikin duba su.

To sai dai wani jami’i a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ya ce Jihar bata da wata matsala da kowanne likita saboda babu wanda ya taba yin korafi a kan yanayin da yake ciki.

%d bloggers like this: