✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

karuwar tashe-tashen hankula

Harin bom din da aka kai wa ginin Babbar Kotun Jihar Ribas, da ke karamar Hukumar Ahoada ta Gabas, inda jami’an ’yan sanda suka bayyana…

Harin bom din da aka kai wa ginin Babbar Kotun Jihar Ribas, da ke karamar Hukumar Ahoada ta Gabas, inda jami’an ’yan sanda suka bayyana cewa ba san wadanda suka kai  harin ba. Wannan al’amari dai ya zama jan kunne ne ga hukumomi kan su yi kokarin shawo kan rikicin da ya baibaye jihar. Kotun wadda ke karkashin jagorancin mai shari’a C.N. Wali, tana gab da yanke wasu mutane hukunci kan uhumarsu da tayar da hankali, wajen yamutsa harkokin siyasa a Jihar Ribas.
A farkon hukuncin, Mai shari’a Wali ya hana daya daga cikin ’yan majalisar jihar Ribas, Mista Ebans Bipi, daga bayyana kansa a matsayin shugaban majalisar. Mista Ebans da wasu mutane biyar suna da hannu dumu-dumu a hargitsin siyasa da aka yi a gaban majalisar, inda aka raunata ’yan majalisar da dama.
Wannan rikicin siyasa wutarsa na kara ruruwa ne saboda hannun shugaban kasa, Goodluck Jonathan da na uwargidansa, Dame Patience Jonathan, inda suke fafatawa kan juya ragamar mulkin jihar a tsakaninsu da Gwamna Rotimi Amaechi.
Su kansu jami’an tsaro, musamman kwamishinan ’yan sanda suna kara dagula al’amura; ta bayyana karara manufarsu ba ta tabbatar da doka da oda ba ce, su kawai so suke yi su biya bukatun son rai na shugabannin siyasa.
A lokacin da wutar rikicin ke ruruwa a bara, an kai hari kan hedkwatar karamar Hukuma, inda aka lalatata..
Daga bisani, rikicin ya mamaye Majalisar Jiha, inda Mista Bipi da wasu mutane biyar suka yi kokarin korar shugaban masu rinjaye, inda suka bullo da wani zama mai sigar wata yaudara, inda suka kaddamar da Bipi a matsayin shugaban majalisar, sannan suka fito da shirin tsige Amaechi daga mukamins ana gwamna.
Rikici ya barke bayan da Amaechi ya jagoranci magoya bayansa, suka kwace karfin ikon majalisar.
Don haka Majalisar Wakilai ta Tarayya ta kwace karfin ikon Majalisar Jihar Ribas; wannan umarni dai wata babbar kotu da ke Abuja ta ce ba shi da tushe a kundin tsarin mulki
Asalin rikicin dai sabanin da aka samu ne tsakanin Amaechi da Jonathan, inda rikicin ya zama barazana ga zaman da tabbatar da doka.
Wasu daga cikin mataimakan shugaban kasa, wadanda suka hada da ministoci suna da hannu tsundum wajen ruruta wutar rikicin.
Wannan mummunan yanayi, yana da hadarin gaske, kamata ya yi Shugaban kasa ya yi amfani da karfin mukaminsa na siyasa, ya hada kan wadanda ba sa ga maciji da juna, don wannan ita ce mafita ga ba ma ga jihar kadai ba, har ma da kasar baki daya.
Bambance-bambancen siyasa bai kamata su haifar da mummunar gaba ba, har ta kai ga kaddamar wa juna munanan hare-hare, inda aka rika lalata gine-ginen gwamnati, wadanda aka kashe makuden kudi wajen gina su.
’Yan sanda sun ce ba su kama kowa ba, a harin bom din da aka kai kotun Ahoada. Wannan kadai abin tashin hankali ne, saboda duk sa’adda rikicin ya shafi wadanda ke da alaka da gwamna nan take da za a kaddamar da kama masu laifin, musamman idan ya shafi wadansu manyan mataimaka ko ’yan siaysar da ke biyayya ga Amaechi, ko da hujjar da aka byar ba ta da inganci
A makon da ya wuce an yi mummunan hadari, inda wata mota da aka ce ta shugaban majalisar Jihar Ribas ce, ta zama abin jefa zargi da munanan kalamai a tsakanin sassan dab a su ga maciji.
Duk da cewa ’yan sanda ba su ce shi ne ke tukin ba a lokacin da hadarin ya auku, duk da haka suka nufi gidansa, suka kama shi bisa tuhumar karya dokokin hanya. Shi sannane ne a gungun masu biyayya ga Amaechi.
Kwanan nan rahotanni suka bayyana cewa an kwace dimbin makamai daga hannun wasu mutum uku da ke da alaka da Uwargidan shugaban kasa. Ba ’yan sanda ne suka kwace makaman ba, jami’an tsaron musamman na STF su suka kai farmaki a yankin. Wasu rahotannin sun nuna cewa ana ta matsin lamba ga jami’an tsaro kan su saki wadanda aka da makaman. Ba za  a iya yin hasashen manufar wadannan masu munanan makamai ba, amma sakin wadannan mutane wauta ce babba, tun kafin a sanar da al’umma manufarsu.
 Ya kuma rage ruwan shugaban kasa, a matsayinsa na babban jami’in tsaron kasa, da ya yi kokarin shawo kan wannan rashin bin doka da oda da ya addabi Jihar Ribas.