✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

KAROTA ta kama mutum 3 kan buga takardun bogi a Kano

Tuni KAROTA ta mika wadanda ake zargin hannun 'yan sanda don fadada bincike.

Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta cafke wasu mutum uku da suka kware wajen buga takardun daukar kaya (Waybill) na bogi.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun hukumar, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, hukumar ta ce mutanen da take zargi da buga takardun dama an jima ana nemansu.

“Hukumar ta dade tana zarginsu da wannan mummunan ta’adar wanda hakan har ya sa aka kara sabunta Waybill din tare da kara masa matakan tsaro.

“Daga cikin wadanda hukumar ta samu nasarar cafke wa sun hada da; Abdulhadi Iliyasu da Shamsu Rabi’u da kuma Samuel Ajayi.”

Ya kara da cewar bayan da aka cafke su, sun bayyana cewa sun dauki sahihiyar takarda guda daya ta hukumar sun kai wa wani mai suna Samuel Ajayi a unguwar Sabon Gari da ke Kanon, domin ya buga musu.

“Bayan da hukumar ta cafke Samuel Ajayi ya tabbatar mata da cewa su suka saka shi ya buga musu Waybill din har sun bayar da kafin-alkalami na Naira 130,000.

“Bayan kammala bincike hukumar ta mika su ’yan sanda don fadada bincike tare da gurfanar da su a gaban kotu,” in ji Kakakin na KAROTA.