✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin ‘yan Najeriya 395 da suka makale a Saudiyya sun dawo

’Yan Najeriya 650 ke nan aka kwaso da su daga Kasa Mai Tsarki inda suka makale

Karin mutum 395 daga cikin ’yan Najeriya da suka makale a kasar Saudiyya sun sauka a Abuja.

Mutnen sun iso ne a ranar Talata cikin jirgin kamfanin Saudi Air a Filin Jiragen Sama na Nnamdi Azikiwe da.

Sawu na biyu ke nan da aka kwaso na ’yan Najeriya da suka makale a kasar. Kawo yanzu, ’yan Najeriya 650 ne aka dawo da su daga Kasa Mai Tsarki.

Hukumar Kula da ’Yan Najeriya da ke Kasashen Waje (NIDCOM) ta ce kafin karshen mako jirgi na uku zai kwaso karin wasu daga Saudiyya.

Hukumar ta ce za a killace mutanen da aka kwaso a sansanin alhazai na Abuja bisa dokar kariyar cutar COVID-19 kafin daga baya su koma ga iyalansu.