Akalla mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano uku ne suka fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP, mai alamar kayan marmari.
Wannan na kunshe ne a cikin wasiku daban-daban da ’yan majalisar suka aike wa Kakakinta, Hamisu Ibrahim Chidari.
- Rarrabuwar kai kan karba-karba ya jawo dage taron PDP
- Wasan kawance: NFF ta bayyana ’yan wasa 30 da za su taka wa Najeriya leda
Uba Abdullahi, wanda shi ne daraktan yada labaran majalisar, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ga manema labarai a Kano ranar Laraba.
Takardun da ke dauke da kwanan watan biyar ga watan Mayun 2022 da aka aike wa Kakakin, ta kuma ce Kakaki ya yi musu fatan alheri kan ficewar tasu.
’Yan majalisar da suka fice daga APC zuwa NNPP sun hada da Abdullahi Iliyasu Yargasa, dan majalisa mai wakiltar mazabar Tudun Wada.
Ragowar sun hadar da Muhammad Bello Butu-Butu, mai wakiltar mazabar Tofa da Rimin Gado da kuma Kabiru Yusuf Ismail, dan majalisa mai wakiltar mazabar Madobi.
Idan za a iya tunawa, ko a makon da ya gabata sai da mambobin Majalisar su tara suka ayyana ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.