✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin mutum 48 sun kamu da cutar coranavirus a Najeriya

Ya zuwa yanzu dai mutum 61,930 cutar Coronavirus ta harbi a duk fadin kasar.

An samu karin mutum 48 da cutar Coranavirus ta harba a fadin Najeriya kamar yadda alkalumar Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Kasar NCDC suka nuna.

Hakan na kunshe cikin sabbin alkaluman da Hukumar NCDC ta fitar a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba, 2020.

Nan da wata biyu za a samu rigakafin COVID-19 –WHO

Cutar coronavirus ta hallaka karin mutum 2 a Najeriya – NCDC

Jihohin da aka samu mutane sabbin kamu sune Legas (18), Abuja (13), Kaduna (6), Ribas (5), Ogun (5), Ondo (1).

Ya zuwa yanzu dai mutum 61,930 cutar Coronavirus ta harbi a duk fadin kasar tun bayan bullarta a watan Fabrairun bana.

Cikin mutum 61,930 da suka kamu da cutar a fadin Najeriya zuwa yanzu, mutum 57,285 sun warke yayin da 1,129 sun riga mu gidan gaskiya.