A kwanakin baya ne Hukumar da ke Kula da Harkokin Wutar Lankarki ta kasa (NERC) ta bayyana cewa ta fara sabbin tsare-tsare ciki har shirin karin farashin wutar lantarki wanda zai fara aiki nan ba da jimawa ba. Ta ce za ta dakatar da tsarin da ake cajan masu amfani da wuta kowane wata ba tare da la’akari da yawan amfani da suka yi ita ba. A yanzu masu amfani da wuta za su biya adadin wutar da suka yi amfani da ita ne kawai. Saboda wannan ne, hukumar ta bukaci Kamfanonin Raba Wutar Lantarki (DISCOs) su fara cajan jama’a bisa abin da suka sha daga mita.
Kodayake, karin kudin ya kunshi karin kashi 48 cikin 100 ga kowane mai amfani da wutar. Amma karin yafi shafar wadanda suke amfani da don tafiyar da harkokin kasuwanci ne, ba wadanda suke amfani da ita a gidaje ba.
Kamar yadda yake a duk lokacin da aka samu karin kuki hakan karin nauyi a kan masu amfani da wutar. Kodayake abu biyu da suka fi damunsu shi ne maganar wadatuwarta da kuma batun mita.
Bayan sayar da kamfanin wutar lantarki na kasa ga ’yan kasuwa, ’yan Najeriya suna sa rai cewa za a samu daidaituwa da wadatuwar wutar. Kodayake, abu ne da kowa ya sani wato har yanzu wutar ba ta wadatu ba. Cajan masu amfani da wutar wadanda ba su da mita lokacin da kamfanin wutar kasar nan yake hannun ’yan kasuwa abu ne mai fuskoki biyu. Yayin da hakan yake hana jama’a damar biyan daidai abin da suka sha na wuta, yana hana kamfanilantarkin damar tattara kudin shigarsu da kuma taimakawa wajen wanzuwar rashawa.
Bugu da kari, akwai korafin da aka dade ana ji wato daga bangaren masu zuba jari kan yadda aka cefanar musu da kamfanonin lantarkin wadanda ba su cancanci su same su ba. Sabon Tsarin Gwamnati na yin Gyara a bangaren Wuta (EPSR) yakamata ya zama wanda zai mayar da hankali ga wadatuwar wutar a duka fadin kasar nan ne. Saboda wannan fata ne kasar nan ta cefanar da kamfanonin ga masu zuba jari. Madadin a samu wutar a kowane lungu da sako na kasar nan, amma sai aka samu karin kudin wutar.
Dalili da wannan ne kungiyar ’Yan kwadago ta (NLC) ta bukaci a dakatar da karin. Kodayake, kungiyar NLC tana kallon matakin karin a matsayin cire tallafi a kan wutar lantarki. Ya dace kungiyar ta duba muhimmancin wadatuwar wutar wanda abu ne da wuya a samu nasara idan aka ci gaba da takaddama a kan janye karin. Mafita a nan shi ne a kara fadada samar da wuta da kuma raba ta. Duk da cewa wannan karin ba zai shafi wadanda suke tsarin R1 (wato masu amfani da wutar a gidaje), ajin da galibin ma’aikatan kasar nan suke ciki.
Wannan karin kudin yana zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin shugabanin gudanarwar hukumar NERC da madakalar kudin sallamar da suka bai wa kawunansu, wanda a yanzu Majalisar Dokoki ta kasa take bincika.
Idan aka yi la’akari da wadannan da ma wasu dalilai na halin da tattalin arzikin kasar nan yake ciki, bai kamata a kara wa masu amfani da wutar kudi ba.
karin kudin wutar lantarki
A kwanakin baya ne Hukumar da ke Kula da Harkokin Wutar Lankarki ta kasa (NERC) ta bayyana cewa ta fara sabbin tsare-tsare ciki har shirin…