Kungiyar Kwadato ta Najeriya (NLC) ta yi wa Gwamnatin Tarayya wankin babban bargo kan batun karin kudin wutar lantarki.
NLC ta caccakin Gwamnatin ne bayan sanarwar da Ministan Wutar Lantarki, Sale Mamman ya fitar da ke cin karo da wadda Hukumar Wutar Lantarki (NERC) ta fitar da farko game da karin kudin wutar daga Naira biyu zuwa Naira hudu.
- Boko Haram ta yi garkuwa da Hakimi a Yobe
- Kotu ta yanke wa matashi hukuncin bulala a Kano
- Hamar: Kabilar da mata ke shan duka kafin a aure su
- Lambar NIN: Ba za a rufe layukan waya ba
“Mun shigo wata shekara kuma da babbar abin da gwamnanti ta sa a gaba shi ne jefa yanayin tattalin ’yan kasa cikin mummunan kangi,” inji kungiyar.
Sanarwar da Shugaban NLC na Kasa, Ayuba Wabba, ta soki sanarwar daMinistan ya fitar daga baya, mai karyata rahotannin da ke nuna an yi karin kudin.
Ayuba Wabba ya ce, tufka da warwarar da ke cikin sanarwan biyu, ya kara tabbatar wa ’yan Najeriya da fargabarsu ta cewa wahalar da suke ciki bata kare ba.