Karin kudin tikitin jirgi da kamfanonin jiragen sama suka yi ya haddasa karancin fasinjoji da ke hawa jirgi.
Wata majiya da ke filin jirgin sama na Murtala Muhammad, ta ce adadin fasinjojin ya ragu sosai tun karshen mako, inda ya ce mutane da dama sun gwammace yin tafiya a mota sakamakon karin kudin tikitin.
- DAGA LARABA: Yadda labaran karya ke buya a tsakanin al’umma
- Kotu ta sahale wa NDLEA ta tsare Abba Kyari na tsawon mako biyu
Wani jami’in daya daga cikin kamfanonin jiragen sama na cikin gida ya ce “Fasinjojin da ke hawa jirgin sama sun ragu. Watakila yanzu mutane sun yanke shawarar bin mota. Wadanda kuke gani a filin jirgin yanzu manyan mutane ne.”
A ranar Talata ce wani ma’abocin amfani da shafin sada zumunta na Twitter, Ikenna, ya wallafa wani hotonsa a cikin jirgi yana zaune da ‘yan tsirarun mutane a ciki.
“Kalli yadda jirgi ya kasance babu kowa a ciki saboda karin N50,000 a matsayin kudin tikiti,” kamar yadda ya wallafa.
Fasinjoji na ci gaba da kokawa kan karin farashin jiragen sama a dukkan sassa na kasar nan.
Sai dai an samu labarin cewa Hukumar Kula da Gasa ta Tarayya (FCCPC), ta ce ba za ta lamunci karin farashin tikitin jirgin ba.
Kazalika, hukumar ta ce nan ba da jimawa ba za ta samar sa matsaya kan takaddamar.
Tun a makon da ya gabata ne, kamfanonin jiragen sama na Najeriya (AON), suka kara farashin jiragen sama da kusan kashi 100 cikin 100 tare da sayar da tikitin zirga-zirga a cikin gida kan kudi N50,000.
Sai dai dora alhakin hakan ne kan karin farashin man jiragen sama wanda ya kusan rubanya har sau hudu, inda yanzu ake sayar da shi sama da Naira 410 kan kowace lita.
Sai dai ga dukkan alamu hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA, ba ta ce komai kan lamarin ba.