Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce karin kudin wutar lantarki da aka yi hukunci ne da aka yanke ba tare da sanin ya kamata ba.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa kan shafinsa na Twitter, a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba.
Wazirin Adamawa ya ce karin kudin wutar lantarkin da gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi a yanzu babu wani hangen nesa a cikinsa.
- Tsohon Ministan Najeriya daga jihar Kano ya riga mu gidan gaskiya
- Yadda ’yan Najeriya ke caccakar karin kudin fetur
Ya ce gwamnatin ba ta yi la’akari da halin kaka-nika-yi da al’ummar kasar ke fafutikar farfadowa daga cikinsa ba sakamakon mummunan tasirin kulle da annobar korona ta haifar.
Ya kara da cewa, ’yan Najeriya sun yi watanni a kulle ba tare da samun wani kudi da yake shigo musu ba.
Ya wallafa cewa; “’Yan Najeriya karfafawa suke bukata a yanzu ba a kawar da ido a kan kalubalen da suke fuskanta ba.
“Wannan karin kudin wuta a yanzu bai dace ba, kuma shawara ce gurguwa”.