Jam’iyyar APC mai mulki ta roki ’yan Najeriya da su kara hakuri su jure karin farashin wutar lantarki da man fetur da aka yi a kwanan nan.
Mataimakin Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar na Kasa, Yekini Nabena ne ya yi kiran a cikin sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata.
- Cire tallafi: Tarihi ba zai manta da Buhari ba – Fadar Aso Rock
- Babu dalilin karin kudin wuta ko mai – Kwankwaso
Ya ce jam’iyyar na sane da wahalhalun da karin zai jawo wa ’yan Najeriya, ya kuma ba su tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za su fara cin gajiyar sabon karin.
Mista Yekini ya ce, “A bangaren alfanu kuwa, karin kudin zai shafi rayuwar ’yan Najeriya saboda irin aikace-aikacen da za su ci gajiya musamman a bangaren lafiya, ilimi, samar da ayyuakn yi da kuma bunkasa rayuwar al’umma”.
Kakakin jam’iyyar ya kuma ce tallafin mai ya lashe kudade sama da Naira tiriliyan 10 daga shekarar 2006 zuwa 2020.
Ya ce abin farin ciki ne yadda ’yan Najeriya suka amince cewa ba da tallafin ba abu ba ne mai dorewa tare kuma da karbar matakin gwamnatin na cire shi hannu bibbiyu.
Mista Yekini ya ce gwamnatoci a baya sun yi ta amfani da harkar bayar da tallafin a matsayin bututun zukar kudaden gwamnati da ya kamata a yi amfani da su a wasu muhimman ayyukan raya kasa.
Daga nan sai ya shawarci kungiyoyin kwadago na TUC da NLC da kada su biye wa kururuwar ’yan adawa a kan matakin na gwamnati mai ci.