Kamfanin Tura da Wutar Lantarki na Najeriya TCN ya ce karfin wutar da ake samarwar a kasar ya kai megawatt 5,420.30 a karon farko a tarihi.
Sanarwar hakan a ranar Alhamis ta ce an turar wutar mai karfin megawat 5,42.30 ne a kan mizanin 50.10Hz daga ranar Talata 18 ga watan Agustan 2020.
“Wannan shi ne adada mafi girma da aka taba samarwa a tarihin [Najeriya]; Ya haura megawatta 5,377.50 da aka samu daga ranar 1 ga Agusta, 2020 a kan mizanin megawatt 42.50”, kamar yadda Jam’in Hulda da Jama’a na TCN Ndidi Mbah ya bayyana.
Sanarwar mai taken ‘An kafa tarihin karuwar wutar lantarki zuwa megawatt 5,420’, ta alakanta samun daidaituwar wutar a Najeriya da yadda gwamnati ta mayar da hankali a kan bangaren.
Ta ce hakan ya faru sakamakon shirye-shiryen da gwamnatin ta kaddamar domin fadada bangaren lantarki da kuma yunkurin masu ruwa da tsaki a kasuwancinsa.
TCN ta kuma bayyana aniyarta na yin aiki kan jiki kan karki wajin ingantawa da kuma daidaitar wutar lantarki a fadin Najeriya.
Ta kara da rokon ‘yan aksa da su ba ta hadin kai ta hanyar bayar da kariya da kadarorinta da ke fadin kasar.