✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kare mai son kai’

Barkanmu da warhaka manyan gobe. Tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amen. A yau na kawo muku labarin wani ‘Kare…

Barkanmu da warhaka manyan gobe. Tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amen. A yau na kawo muku labarin wani ‘Kare mai son kai’. Labarin yana nuni ga illar son kai da kuma yadda rowa ke janyo yin nadama. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi.

Akwai wani kare mai yawan son kansa sannan ga rowa. Sau dayawa wannan abin na janyo masa kunya a cikin sauran ’yan uwansa har abin ya kai ga yi wa kansa fada ya canza hali domin shi kansa abin na damunsa.
Rannan yunwa ta dame shi sai ya tafi wani wuri domin neman abinci. Ya shiga sunsune-sunsune can sai ya ci karo da wani katon kashi mai dan nama a jikinsa. Har ya sunkuya zai fara ci sai ya tuna cewa wani karen zai iya tarar da shi kuma dole su raba.  Daga nan ya yanke shawarar tafiya gida don ya boye ya ci shi kadai a hankali ba tare da wani ya ganshi ba.
A hanyarsa ta komawa gida sai ya hau wata gada, a kasan gadar kuma akwai ruwa. Can sai ya ga hangi wani Karen a cikin ruwa yana rike da kashi irin nasa. Bai san cewa wannan karen inuwarsa ce ba.
Sai ya ce bari ya kwato wannan kashin a hanun Karen nan saboda ya samu kashi biyu. Yana cikin haushi sai kashin bakinsa ya subuce ya fada cikin ruwa. A lokacin ne ya gane cewa ashe inuwarsa ce a ruwan ga shi kuma ya yi asara.  Da haka dai ya yi biyu babu.