✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karbuwar Buhari ga ’yan Najeriya

Yakin zaben Shugaba Buhari da ya gudana a jihohin Najeriya hakika ya ba mu matukar mamaki. Hakika muna mamakin yadda mutane ke kara son Shugaba…

Yakin zaben Shugaba Buhari da ya gudana a jihohin Najeriya hakika ya ba mu matukar mamaki. Hakika muna mamakin yadda mutane ke kara son Shugaba Muhammadu Buhari musamman a wannan lokaci da Shugaban ya yi yakin neman zabe karo na biyu. Duk inda shugaba Buhari ya je za ka ga dimbin mutane kamar su cinye kansu sun yi dandazon don tarbarsa, tabbas haka ya nuna wa duniya cewa Shugaba Buhari ya  karbu a wurin jama’arsa don haka nasarar da ya samu a zaben makon jiya ba ta ba kowa mamaki ba.

Sai dai kuma babban kalubale ga Jam’iyyar APC da al’ummar kasa shi ne yayin da Shugaba Buhari ke kara samun farin jini da tagomashi a idon ’yan Najeriya wane ne Buhari na biyu idan Shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa karo na biyu n Allah Ya bashi ikon kara lashe a shekarar 2023?

Ba na tunanin Jam’iyar APC za ta kara samun wani dan takarar da zai kama kafa  Shugaba Buhari wajen farin jini da karbuwa. Idan yau babu Shugaba Buhari,  tabbas Jam’iyyar APC a Najeriya za ta shiga matsala. Don haka ina kira ga ’ya’yan Jam’iyyar APC su zama adalan mutane kamar Shugaba Buhari domin lokacin da babu shi su taka irin rawar da yake takawa.

Daga Abba Sa’ad Mahuta, 08107130655.