✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karbar cin hanci: An dakatar da DCP Abba Kyari daga aiki

Hakan na da alaka da zargin da ake masa cikin damfarar da Hushpuppi ya yi.

Babban Sufeton ’Yan Sanda na kasa, Usman Alkali Baba a ranar Lahadi ya bayar da shawarar dakatar da dan sandan nan, DCP Abba Kyari daga aiki.

Hakan na da alaka ne da binciken da ake masa kan zargin da Hukumar Leken Asiri ta Amurka (FBI) ta yi masa na hannu dumu-dumu a cikin zargin wata badakalar kudade da ake wa wani dan damfara mai suna Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi, ko da dai ya sha musanta zargin.

FBI ta kuma roki hukumomin Najeriya da su kama Kyarin saboda yadda ya taka rawa a cikin badakalar, musamman wajen kulle daya daga cikin abokan huldar Hushpuppin.

Umarnin korar dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar ta kasa, Frank Mba ya fitar ranar Lahadi wacce ta ce Babban Sufeton ya ba da umarnin dakatar da shi har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kansa.

Sanarwar ta ce, “Babban  Sufeton ’Yan Sanda, Usman Alkali Baba ya amince da shawarar korar DCP Abba Kyari, shugaban Sashen Leken Asiri na rundunar ba tare da bata lokaci ba daga aikin dan sanda har zuwa lokacin da za a kammala binciken da ake a kan shi.

“Babban Sufeton a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 31 ga watan Yulin 2021, ya ce dakatarwar na cikin tanade-tanaden rundunar na ladabtarwa.

“Za kuma ta bayar da dama a gudanar da cikakken bincike kan babban zargin da ake yi masa ba tare da samun katsa-landan ba.

“Kwamitin binciken ya kunshi mutum hudu, karkashin jagorancin Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda, DIG Joseph Egbunike, wanda Mataimakin Insfekta ne mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuffuka (FCID) na rundunar.

“Binciken kwamitin zai gano gaskiyar dukkan zarge-zargen da ake yi wa DCP Abba Kyari ko akasin haka, ya gano gaskiyar lamarin yadda ya kamata, sannan ya mika shawarwarinsa wadanda da su ne rundunar za ta yi amfani da su wajen daukar mataki.

“Babbn Sufeton na tabbatar da cewa za a bi doka da oda da tabbatar da yin adalci a binciken cikin mutuntawa da kiyaye hakkin dan Adam har zuwa kammala shi.