Wani malamin addinin musulunci daga Jihar Kano, Malam Muhammad Musa Nazir, ya bayyana tsarin karatun allo a matsayin mafi dacewa wajen yin haddar alkur’ani fiye da hanyar zamani da ake bi yanzu a makarantun Islamiyya.
Malam Nazir, ya bayyana hakan ne a Gombe a lokacin da ya je bikin saukar karatun makarantar Al-Jawda Islamiyya ta daya daga cikin dalibansa da suka yi karatu a gabansa a Kano.
- Mun kori Sheikh Nuru Khalid daga limanci gaba daya —Sanata Dansadau
- CBN zai hukunta bakunan da ke karbar yagaggun kudi
“Ita wannan hanyar ta na yi amma gaskiya bata bullewa sosai domin ba a bin ka’idojin da suka kamata kamar na tsarin karatu da allo wanda ba yadda za a yi ka wanke allon ka sai ka haddace abin da ke rubuce a jiki.
“Idan so samu ne a hadu a fito gaba daya a yi gyara wajen inganta tsarin karatun allo na taimaka wa malaman tsangayu saboda su ne suke kan tsarin mafi bullewa”.
Shi dai Malam Muhammad Musa Nazir, hafizi ne wanda yanzu haka ya rubuta alkur’ani sau 62 da hannunsa.
Ya ce hanyar da magabatan mu suka bi wajen yin karatu da allo shi ne kawai za a bi a samun hadda ingantacciya.
A cewarsa a bai wa malaman tsangayu abun yi su samu hanyar dogaro da kans,u hakan zai sa su tsaya sosai wajen koyar da yara, sannan iyaye su ba da kudin abincin ‘ya’yansu da hakan zai hana su yin bara su dinga kai musu omo da sabulun wanka da wanki don kar su dinga zama cikin datti.
Ya kara da cewa, a dinga bai wa malami almajirai ‘yan dadai ba masu yawa da za su fi karfin ya shawo kai ba.
Kazalika, ya ce karatun allo ne kadai zai baka dama na sanin adadin bakake da harrufan alkur’ani ba kamar mai karatu da littafi ba.
Malam Nazir, ya ci gaba da cewa har yanzu haka yana karatu da allo, inda a kullum ya ke rubuta izu biyu a allunansa guda bakwai.
Sannan ya ce ko da mace ce ta yi aure, yana da kyau a kaita gidan miji da allonta na hadda, mijin ta zai fi alfahari da ita a kan a kaita da wata takarda mai rubutu da sunan wai ita mahaddaciya ce.