Minista a Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur Dokta Emmanuel Ibe Kachikwu ya nemi afuwar ’yan Najeriya kan yadda ya ce ba zai iya dabo wajen magance matsalar karancin man fetur da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar nan ba.
Dokta Ibe Kachikwu ya nemi afuwar ce a wajen wata ganawa da Kwamitin Harkokin Man fetur na Majalisar Dattawa a ranar Litinin da ta gabata a Abuja, inda ya ce ya yi nadamar furta kalmar ‘dabo’ a cikin maganganunsa inda ya ce bai yi haka domin ya ci zarafin ’yan Najeriya ba.
“Ina neman afuwa kan wannan kalami da na yi, kuma na yi ta ne don raha da abokaina ’yan jarida cewa ba zan iya dabo ba. Ban yi nufin cin zarafin ’yan Najeriya ba. Ban san hakan zai jawo cece-ku-ce ba. Ina son shaida wa jama’a ni ba kwararren dan siyasa ba ne, ni ma’aikaci ne. Wasu kalmomi da zan yi amfani da su, yayin da za su iya karbuwa a wuraren da na kware, ta yiwu ba za su karbu a wurin jama’a ba. Don haka idan akwai wanda yake jin na saba masa ta wannan furuci to ina neman afuwarsa,” inji Kachikwu.
Dokta Kachikwu ya ce yana aiki wurjanjan domin samo maslaha ta dindindin don kawo karashen wahalar mai a kasar nan, kuma ya tabbatar wa ’yan Najeriya nan da mako na daya ko na biyu na watan Afrilu za a yi ban kwana da wahalar mai domin Kamfanin Mai na kasa (NNPC) yana yin duk abin da ya wajaba domin wadata kasar nan da mai.
Ya bayyana cewa Kamfanin NNPC, yana aiki domin zamanantar da sassansa ta yadda za su iya gano yadda ake rarraba mai tun daga daffo zuwa gidajen mai.
Dokta Kachikwu ya nanata cewa yana kokarin tsabtace kazantar da ya samu kamfanin man ne a hankali domin samar da kafar gudanar da aiki bisa nagarta. Sai ya ce ba zai sauka daga mukaminsa ba, kamar yadda wasu suka nema, inda ya ce zai ci gaba da aiki domin inganta harkokin mai na Najeriya.
karancin mai: Kachikwu ya nemi afuwa kan ba zai iya ‘dabo’ ba
Minista a Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur Dokta Emmanuel Ibe Kachikwu ya nemi afuwar ’yan Najeriya kan yadda ya ce ba zai iya dabo wajen magance…