✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

karancin mai ba zai jawo karin kudin mota ba – kungiyar NARTO(1)

kungiyar Direbobin Sufuri ta NARTO reshen karamar Hukumar Katsina ta ce karancin man fetur ko ba zai sanya su kara wa fasinjoji kudin mota kamar…

kungiyar Direbobin Sufuri ta NARTO reshen karamar Hukumar Katsina ta ce karancin man fetur ko ba zai sanya su kara wa fasinjoji kudin mota kamar yadda wasu suka yi tsammani.
Mataimakin Shugaban kungiyar Alhaji Alah Mohammad Katsina ne ya shaida wa Aminiya, inda ya nuna damuwarsa a madadin kungiyar a kan yadda karancin mai ya nemi kassara harkokin sufuri ba wai a jihar da kuma wasu yankunan kasar nan.
“Ganin irin kokarin da gwamnatin jiha ke yi na ganin ta kawo saukin sufuri ya sa muma kungiyarmu ta bi wannan sahu na bayar da tata gudunmuwar. A kan haka ne, farashin da ake biya a motocin gwamnati irin shi ne muke karba. Kuma motocinmu suna zuwa ko’ina a cikin kasar nan bisa wannan farashi irin na gwamnati. Wannan kuma haka yake tun kafuwar wannan kungiya a jahar nan har ya zuwa yau,” inji shi.
Har ila yau, ya yi kira ga matafiya da su guji shiga mota a wuraren da ba tashar mota ba ne “saboda kiyaye lafiyarsu da ta dukiyoyinsu.”
Ya kara da cewa “shiga mota a cikin tasha yana da fa’idoji da yawa, kadan daga cikinsu sun hada da rashin bacewar kayan fasinja idan ya manta su a mota saboda ko a yanzu haka akwai irin wadannan kaya na mantuwa a ma’ajiyarmu wadanda da zarar mun tabbatar da mai shi za mu ba shi abinsa.”
A karshe ya bukaci direbobi da su zamo masu bin doka da oda duk inda suka samu kansu.