Sri Lanka za ta rufe ofishin jakadancinta a Najeriya saboda ta rage kashe kudin gudanarwa da kuma adana dalar Amurka da take matukar bukata a halin yanzu.
BBC ya ruwaito Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar tana cewa za ta rufe babban ofishin jakadancinta a Najeriya sannan ta rufe wasu kanana a Jamus da Cyprus.
- An rufe makarantu kan tsammanin harin ’yan bindiga a Neja
- Matsalar tsaro: Mabiya Darikar Kadiriyya sun gudanar da addu’o’i na musamman
A zantawarsa da jaridar Daily Mirror, Ministan Harkokin Wajen Sri Lanka, Farfesa Gamini Lakshman Peiris ya ce kasarsa za ta mayar da ayyukan ofishin jakadancinta da ke Frankfurt a Jamus zuwa birnin Berlin.
Ya ce ofishin jakadancinta na Najeriya zai kuma ci gaba da aiki ta hannun ofishin jakadancinta da ke kasar Masar.
A makon jiya ne Majalisar Ministoci ta tattauna kan karancin dalar Amurka da kuma matsin tattalin arziki da ta fuskanta a rubu’i na uku na bana, lamarin da ya sanya ta shimfida matakan da za a bi domin tufkar hanci.
Ana iya tuna cewa, a shekarar 2017 ne Najerita ta rufe ofishin jakadancinta da ke birnin Colomba a Sri Lanka, matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai sake duba shi.