✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

karancin albashi shi ne matsalarmu a Jihar Barno

An sayo kare domin haushi, amma ya bige da kukan akuya. Aminiya mai farin jini domin Allah ku mika mini sakona zuwa ga gwamnan Jihar…

An sayo kare domin haushi, amma ya bige da kukan akuya. Aminiya mai farin jini domin Allah ku mika mini sakona zuwa ga gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima shin ina aka kwana ne game da karin kudin albashin kananan ma’aikata?

Tsawon shekaru hudu ke nan kana kan mulki, amma ka ki daukar sabbin ma’aikata, ka ki karawa kananan ma’aikata
albashi. Haba gwamna wannan shi ne shugabanci? Sanin kowa ne kaf fadin Najeriya babu jihar da kananan ma’aikatanta suke karban naira dubu takwas da sunan albashi, sai a Jihar Barno.
A gaskiya mufa a yanzu an shamu mun warke, domin haka lokaci ya yi da za ka yiwa ma’aikata karin albashi. Sabili da a yanzu dai lokaci ya yi da zamu fito mu bayyana wa duniya halin da gwamnanmu ya sanyamu a ciki. A gaskiya da kunya ace ana yabon ka sallah, amma alwala ta gagare ka. Babban kuskure ne kana alakanta matsalar rashin tsaro da ta addabi al’ummar jihar ka ce sai an samu sa’idar rayuwa sa’annan za ka yiwa ma’aikata karin albashi. To wallahi ya kamata ka kwana da sanin cewa, idan maye ya ci ya manta, uwar da bata manta ba. A karshe ina rokon Allah Ya ganar da gwamna Kashim Shettima sanin nauyin hakkin talaka. Domin kuwa duniya dai gidan jarrabawa ne, watan wata rana sai tarihi.
Daga Adamu Aliyu Ngulde, Dambo’a, Jihar Barno, 08032135939.

Kan zanga-zangar masu rini a Kano

Assalamu alaikum, zan yi tsokaci ne akan zanga-zangar da masu sana’ar rini suka gudanar a birnin Kano, inda suka kaiwa mai girma Sarkin Kano ziyara tare da kuken cewa yakamata gwamnatin jihar ta shiga tsakani akan ‘yan kasuwar China da ‘yan kasuwar Kano masu sana’ar rini wadanda ‘yan kasar China ke kokarin kwace musu sana’arsu ta rini ganin yadda kasuwancinsu ke dab da durkushewa sanadiyyar shigowa da rinannun kaya da ‘yan kasuwar China ke shigowa da su, don haka muma ‘yan Najeriya muna matukar goyan bayan wadannan ‘yan kasuwa wadanda suka gudanar da zanga-zangar lumana don samo musu hakkinsu da fatan gwamnatin jihar za ta yi abin azo a gani akan wadannan ‘yan kasuwar masu neman hakkinsu. Daga karshe muna addu’a Ya Allah ka kawo ma kasarmu zaman lafiya.
Daga Kwamared Nura Bello, Jihar Zamfara, 08032558025.

Yakamata hukumin Jihar Kano su yi duk mai yiyuwa wajen ganin cewa sun taimaka ma kananan ‘yan kasuwa, musamman marina domin kaucewa duk wata durkushewar harkokin kananan masana’antun sakamakon shigo wa da kaya daga wasu kasashen ketare.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi, Gusau, 08069807496.

Kan ziyarar Shugaban Chadi a Najeriya
Salam, hakika ziyarar Shugaban Chadi Idiris Deby a Najeriya, inda ya gana da Shugaba Goodluck Jonathan mai barin gado, inda yake cewa wai rashin hadin kan jami’in tsaron kasar nan da na kasarsa ne ya jawo tsaikon kauda masu tada kayar baya, ba abin mamaki ba ne domin kai da kanka ka ce za ka kamo Abubakar Shekau, amma har yau shiru muke ji kamar an shuka dusa.
Daga Hafizu Balarabe Gusau, 07035304499.

Masari alkawari kaya ne
Da farko ina son na yi amfani da wannan dama na mika sako ga sabon gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, wanda shi ma idan aka duba tarihi ya cancanci a jinjina mai ta fuskar hakuri da juriya, inda fiye da sau biyu ya nemi wannan matsayi, amma mai kowa da koma ya tabbatar da shi a wannan lokacin.
Hakazalika, ga ’yan majalisu da dama masu kima da ake kallon abokan shawara managarta to domin Allah adai duba matsalolin rashin aikinyi ga matasa, a kula domin a lokuttan yakin neman kuri’u an yi ma al’ummar Jihar Katsina musamman matasa fatan samun abin yi wanda ayau a dalilin rashin abin yi, sai zaman kashe wando.
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina, 07066434519.

Akwai manya kalubale a gaban gwamnati mai jiran gado
A gaskiya akwai manya kalubale a gaban gwamnati mai jiran gado da suka hada da: cin hanci da rashawa da rashin ayyukkanyi da rashin samun isasshiyar wutar lantarki da matsalar tsaro da dai sauransu. Saboda haka ya kamata gwamnati mai jiran gado, ta dauki matakin magance wadannan matsaloli da zarar ta kama mulki, domin ci gaban kasarmu Najeriya da kuma dawo mana da martarbar kasarmu a idon duniya, kamar yadda aka santa a da. Har ake mata kirari da “Giwar Afirka”.
Daga Aminu dan Kaduna Amanawa, 09035522212.