Wani karamin yaro mai wata 19 ya fada a rijiya a gidan da aka kai shi raino a Karamar Hukumar Dambata ta Jihar Kano.
Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne bayan kakar yaron da aka kai wa rainon shi ta bar shi ya yi wasa a farfajiyar gida shi kadai.
- Jamus ta kara wa Ukraine makamai masu linzami 2,700
- Hajji 2022: NAHCON ta umarci hukumomin alhazai su fara shiri
Rahotanni sun bayyana cewa yaron wanda iyayensa suke garin Minjibir sun kai shi raino ne a wajen kakarsa da ke zaune a Dambatta.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa hukumar ta samu kiran neman agaji daga wani mai suna Salisu Bello kuma nan take suka tura jami’ansu zuwa wurin.
Ya ce bayan an shiga rijiyar don ceto yaro, an samu ya riga ya rasu sakamakon shan ruwa da ya yi a cikin rijiyar.
A cewarsa, “Jami’anmu sun ciro gawarsa daga rijiyar kuma mun fara bincike kan abin da ya faru,” amma tuni aka mika gawar ga kakan mamacin, Malam Abdulkadir don yi masa sutura.
Kakakin hukumar ya kuma ja hankalin iyaye da su kasance masu lura da yaransu don gujewa faruwar irin hakan.