✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kansilolin Edo 90 sun roki Buhari ya tursasa Obaseki ya biya su albashinsu

Zababbun kansiloli 90 karkashin jam’iyyar APC a Jihar Edo sun bukaci Shugaba Buhari da Shugaba Kwamitin Rikon Jam’iyyar, Mai Mala Buni da su tursasa Gwamna…

Zababbun kansiloli 90 karkashin jam’iyyar APC a Jihar Edo sun bukaci Shugaba Buhari da Shugaba Kwamitin Rikon Jam’iyyar, Mai Mala Buni da su tursasa Gwamna Godwin Obaseki ya biya su albashinsu da ya rike na wata biyar.

A tattakin da suka yi zuwa sakatariyar jam’iyyar domin mika wasikar kokensu a ranar Laraba, kansilolin da Honorabul Enwinghare K. Osabuohie ya jagoranta sun ce jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ta kasa jure wa adawa.

“Ya kamata duniya ta sani, a matsayinmu na zababbun kansiloli mu fiye da 90, an rike mana albashi tun watan Mayu, 2020.

“Albashin ’yan majalisa ba kyauta ba ce da masu mulki suke ba su. Gwamna Obaseki ya sa an tsayar da duk wani hakki da ya kamata mu karba a matsayin zababbu.

“Laifin mu shi ne mun ki sauya sheka tare da shi zuwa jam’iyyar PDP saboda mun auna aikin da ya yi wa mutane kuma muka fahimci babu dalilin da za mu bar jam’iyyar da ta ba mu dama aka zabe mu.

“A jihar, an kori ma’aikata da dama zababbu da wadanda aka dora a kananan hukumomi 16 cikin 18. Majalisar dokokin jihar a yanzu haka an nakasa ta,”

Tun da farko Gwamna Obaseki ya karyata zargin ta bakin mai magana da yawunsa, Crusoe Osagie.

“Zargin da wasu ke yi na cewar suna bin albashi ba shi da tushe. Zargin cewa an ki biyan su albashi saboda bambanci  siyasa ya fi muni. Duk zarge-zargensu karya ne kuma ba su da tushe”, inji shi.