Kansilan Mazabar Guringawa a Karamar Kukumar Kumbotso ta Jihar Kano ya nada hadimai 18 da za su mataimaka masa wurin gudanar da harkokin yankin.
A wasikar nadin hadiman da Aminiya ta gani, Kansilan Guringawa, Muslihu Yusuf Ali ya ce za su taimaka masa ne wajen sauke nauyin da ke kansa a wasu fannoni na tabbatar da cigaban yankin.
- Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba —Monguno
- Na koya wa Ameachi darasi a siyasa —Wike
- An rufe makarantun sakandaren gwamnati a Neja
“Ina sanar da jama’a nadin mataimakan da za su taimaka min wajen sauke nauyin da ke wuyana a fannoni daban-daban na tabbatar da ci gaba, walwala, tsaro da kuma jin dadin al’ummar Guringawa,” inji sanarwar.
Aminiya ta gano cewa a ranar Alhamis 11 ga watan Maris, 2021 ake kaddamar da hadiman a Sakatariyar Karamar Hukumar Kumbotso.
Daga cikin wadanda aka nada akwai:
- Sulaiman Ibrahim Bako, Mataimaki na Musamman
- Yahaya Abdu Yahaya, Babban Sakatare na Musamman
- Kamalu Garba LY, Kafafen Watsa Labarai na Zamani
- Usama Umar Zubair, Mashawarci na Musamman kan Harkokin Addini.
Sauran mukaman su ne:
- Mashawarci kan Tallafi da Harkokin Jinkai
- Mashawarci kan Kafafen Sa Da Zumunta
- Mashawarci kan Kungiyoyi Masu Zaman Kansu da Zuba Jari
- Da kuma Mashawarci kan Harkokin Siyasa da sauransu.