Nan ba da dadewa ba Jihar Kano za ta fara gudanar da wasannin ’yan kasa da shekara 13 (U-13) da kuma na ’yan kasa da shekara 15 (U-15).
Wasannin wanda Shugaban Hukumar Wasan kwallon kafa ta Jihar Kano zai duki nauyin gudanarwa za a yi masa take ‘Ahlan U-13 da U-15 championship”.
Ahlan ya bayyana cewa hukumarsa za ta hada kai da kungiyoyin kwararru a fadin jihar don a kafa kungiyoyin U-13 da na U-15 wadanda za su rika shiga gasar wacce za a rika gudnarwa bayan duk watannin shida-shida.
Ahlan ya kara da cewa “a karshen lokacin wasannin za a fitar da wadanda suka nuna kwazo tare da zabensu don su wakilci jihar a gasar wasan Zenith U-13 da U-15 a matakin kasa.”yan kasa da shekara 15 (U-15).
Wasannin wanda Shugaban Hukumar Wasan kwallon kafa ta Jihar Kano zai duki nauyin gudanarwa