✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano Pillars ta kafa sabon tarihi

A karshen makon jiya ne kulob din kwallon kafa na Kano Pillars da ke Kano wanda ake wa lakabi da “ Sai Masu Gida” ya…

A karshen makon jiya ne kulob din kwallon kafa na Kano Pillars da ke Kano wanda ake wa lakabi da “ Sai Masu Gida” ya kafa sabon tarihi bayan  ya lashe gasar rukuni-rukuni na Najeriya a karo na biyu a jere, kuma sau uku a tarihin kulob din.
Kodayake kulob din Lobi Stars da ke Makurdi ya doke na Pillars da ci 2-0 a wasan karshe a ranar Lahadin da ta wuce, duk da haka kulob din ne ya samu nasarar lashe gasar bayan ya hada maki 63 daga cikin wasanni 38 da ya yi.
Bayelsa United ce ta kasance ta uku bayan ta hada maki 61 yayin da El-Kanemi Warriors ta zama ta hudu da maki 60.
Kano Pillars ta kasance kulob din da ya taba lashe gasar sau biyu a jere tun kimanin shekaru goma da suka gabata bayan da kulob din Enyimba ya lashe sau biyu a jere a kakar wasa ta 2001 zuwa 2002 da kuma ta 2002 zuwa 2003.
A halin yanzu Pillars da Enyimba ne za su wakilci Najeriya a gasar neman cin kofin zakarun kulob-kulob na Afirka da za a yi a badi.
Kulob din da suka samu koma baya (relegation) a gasar rukunin Najeriya sun hada da ABS FC da ta Kwara United da Wikki Tourist da kuma na Shooting Stars da ke Ibadan.

….dan kwallon Nasarawa United bictor Namo ne ya lashe takalmin zinare a gasar

Dan kwallon Nasarawa United Victor Namodan kwallon gaba a kulob din Nasarawa United mai suna bictor Namo ne ya samu nasarar lashe kyautar takalmin zinare (Golden Boot) a gasar rukuni-rukuni na Najeriya da ake wa lakabi da Nigeria Professional Football League, NPFL) bayan da ya zura kwallaye 18 a gasar da aka kammala a karshen makon jiya.
Namo wanda ya sha alwashin zura kwallaye 20 a farkon gasar amma ya kare da zura kwallaye 18, shi ya zura kwallo a ragar kulob din Heartland a ranar Lahadin da ta wuce a wasan karshe. Nasarawa United ce ta samu nasara a wasanta da Heartland da ci 1 babu ko daya.
Wannan nasara da Nasarawa United ta samu ya sanya ta kasancewa daya daga cikin kungiyoyin da za su cigaba da fafatawa a gasar a kakar wasa mai zuwa, ma’ana kulob din ya tsallake tarkon fadawa koma-baya a gasar (relegation) kenan.
Tsohon dan kwallon Kano Pillars, Namo ya bayyana wa kafar sadarwar supersport.com a ranar Litinin da ta gabata cewa ya yi matukar farin ciki kasancewa kulob din Nasarawa United ya tsallake fadawa tarkon koma baya (relegation) kuma da kasancewarsa dan kwallon da ya lashe kyautar takalmin zinare a gasar.
Nasarawa United ta kasance ta 13 daga cikin jerin kungiyoyin kwallon kafa 20 da suka fafata a gasar bayan ta hada maki 52 daga cikin wasanni 38 da ta yi.