✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano Pillars da Katsina United sun koma gasar Firimiya ta kasa

A kakar bara aka koro kungiyoyin biyu

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da takwararta ta Katsina United sun sami damar komawa gasar Firimiya ta kasa.

Hakan na zuwa ne duk da Katsina United ta lallasa Kano Pillars ranar Laraba da ci 1-0 a gasar kwallon kafa ta Najeriya (NNL), a filin wasa na Stephen Keshi da ke Asaba, babban birnin Jihar Delta.

Kungiyoyin biyu dai sun gaza kai bantensu zuwa Firimiyar ne a kakar wasanni ta bara.

Kafin nan dai, Kano Pillars ta samu nasarar zuwa matakin ne bayana ta lallasa kungiyar DMD da ke Jihar Borno da ci 2-0, kwana daya bayan kuma ta lallasa kungiyar EFCC.

Da wannnan nasarar dai, yanzu da Kano Pillars da Katsina United duk sun cancanci shiga gasar ta Firimiya da maki shida-shida, amma Katsina ce a kan gaba saboda ta fi Kano da yawan kwallaye.

Idan za a iya tunawa, tun a kakar wasa ta 2021/2022 ne Kano Pillars ta gaza kai bantenta a neman gurbin shiga gasar ta Firimiya, lokacin da kungiyar ta fada tsaka ma wuya.

Kungiyoyi hudu ne daga cikin takwas din da suka rage a gasar za su wakilci Najeriya a gasar zakarun nahiyar Afirka ta kakar bana.

Tuni dai kungiyar Sporting Legas ta sami gurbin shiga gasar kafin Kano da Katsinan.