Wata matar aure ta gurfanar da mijinta a gaban Kotun Musulunci da ke unguwar Dorayi a Jihar Kano, tana neman rabawa da shi kan rauninsa da rashin karfafa mata gwiwa wurin kula da da yaransu 10 da suka haifa.
Matar ta shaida wa kotun cewa “mijina malalaci ne na yankan shakku, ba ya kuma sauke nauyin da ke kansa na maigida saboda ba abin da yake mana.
- Kansila ya nada mataimaka 18 a Kano
- Ya kamata sojoji su bi Boko Haram har maboyarsu —Majalisa
- Ba zan iya kaskantar da kaina zuwa matakin Wike ba —Raddin Amaechi
“Ba ya kula da abin da ya shafi lafiyarmu, dawainiyar gida, ilimi ko samar da abinci.
“Yana zaune ne a gidana ba tare da tabuka komai ba, ni ke daukar dawainiyar gida da sauran bukatunmu baki daya,” inji ta.
Bayan kammala jin korafe-korafenta, alkalin kotun, Malam Umar Dan-baba ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Mayu, 2021.