Tun da aka kirkiro Jihar Kano a 1967, ba a taba samun matar Gwamna mai karfin fada-a-ji ba a sha’anin tafiyar da gwamnati irin matar Gwamna mai ci, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ba, wadda a birni da karkara aka fi sani da Gwaggo.
Matar da sannu a hankali karfin fada-a-jinta yake kara bayyana a kullum a jihar.
Zuwa yanzu dai an yi gwamnoni 18 a jihar, goma na mulkin soja, takwas na farar hula.
Irin wannan karfin fada-a-ji na Gwaggo, ba a boye yake ba a lungu da sakon jihar, al’amarin da ya kai matsayin duk ma’abucin sauraren kafofin yada labarai a jihar, kusan a kullum zai ji irin yadda masu koke-koken da suke son gwamnatin jihar ta biya musu bukatunsu, sukan roki Gwaggo ta sa baki a kan Gwamna Ganduje ya share musu hawayensu.
Hatta masu neman a nada su mukami kowane iri a jihar ko neman wata kwangila da sauran alfarma daga Gwamna Ganduje ko gwamnatinsa, da zarar sun bi ta kan Gwaggo, to kuwa ba makawa bukata za ta biya.
Irin karfin da Gwaggo take da shi a Gwamnatin Jihar Kano, ya sa a jihar ake ta zargin Gwamna Ganduje da zama MijinTa-Ce, kasancewar duk abin da Gwaggo ta ce a yi a gwamnatin jihar ba ya faduwa kasa banza.
Ko nade-naden da aka yi wa mata a matsayin kansiloli a dukkan kananan hukumomin jihar 44 a ’yan watannin baya, Gwaggon ce ta ce lallai a yi.
Yanzu haka kowace Karamar Hukuma a jihar tana raba tallafin kudi ko jari ga mutanen jihar, tallafin da ake zargin daga Naira miliyan goma-goman da sanannen attajirin nan kuma mai taimakon al`umma da addinin Allah na Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya ba kananan hukumomin a ’yan watannin baya da sunan su je su fara aiki bayan zabensu.
Inda duk aka raba tallafin zuwa yanzu Gwaggo ke raba shi da kanta kuma adadin mata kan fi na maza yawa a cikin masu amfana da tallafin kuma rabonsu (matan) yakan fi na maza yawa.
A cikin irin ayyukan da Gwaggon take yi ne a kwanan nan aka ruwaito ta tana bayyana cewa sun samu wanda zai gaje su, ma’ana ta yi nunen wanda zai gaji mijiinta a kan karagar mulkin jihar a shekarar 2023, in Allah Ya kai mu.
Wanda ta nuna shi ne Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, wanda ake yi wa lakabi da KWAMANDA.
A fadarta, Kwamanda jajirtacce ne wajen gudanar da ayyukan gwamnatin jihar kuma haziki ne mai tsananin biyayya gare su, don haka shi ne magajin maigidanta a shekarar 2023, in Allah Ya kai mu.
Jin wadancan kalamai na Gwaggo ke da wuya sai ga martanin gwamnatin jihar ta hannun Kakakinta kuma Kwamishinan Watsa Labarai, Malam Mohammed Garba, inda ya ce abin da Gwaggon ta fada, ba wai an yi ke nan ba.
Yana mai cewa shauki a kan gamsuwa da irin yadda Kwamishina Murtala yake gudanar da ayyukansa ne ya sanya Gwaggon ta yaba masa kamar yadda takan yaba wa sauran jami’an gwamnati da ta gamsu da kwazonsu, amma sam ba tana nufin Kwamandan ne magajin Gwamna Ganduje ba.
Kamar kowane muhimmin ra’ayi irin wannan da wani da ya isa a gwamnati yakan furta yake, samun mabanbantan ra’ayoyi na fahimta, shi ma kalaman nunen na Gwaggo haka ya kasance ga wadansu mutanen jihar.
Yayin da wadansu suka yi imani cewa nunen na Gwaggo a kan Kwamishina Murtala haka yake, lokaci kawai ake jira ya tabbatar da shi, bisa ga irin karfin fada-a-jin da irin wadancan mutane suka san Gwaggon tana da shi a gwamnatin mai gidanta.
Wadansu kuma suna da ra’ayin cewa nunen da Gwaggon ta yi, ta yi ne don ji da gane ra’ayoyin jama’ar jihar, musamman masu ruwa-da-tsaki a Jam’iyyar APC.
Dukkan masu wadannan ra’ayoyi sun hakikance cewa bisa ga matsayin shekaru da ilimi da wayewa da gogewa da gwagwarmayar da Gwoggo take da su a rayuwa, sun wuce a ce da gangan ko da ganganci ta yi wancan nune a kuma bainar jama’a.
Ko a ’yan kwanakin nan Gwamna Ganduje, a karon farko a wani taron bude wa Gwaggon ofishin da za ta rika gudanar da ayyukanta na Matar Gwamna, ya mayar da martani ga masu kiransa “Mijin-Ta-Ce” inda ya ce shi ba “Mijin-Ta-Ce” ba ne, shi “Mijin-Kan-Ta-Ce” ne.
Tabbas wannan furuci na Gwamna ya kara tabbatar wa jama’a irin karfin fada-ajin da Gwaggo take da shi wajensa da cikin tafiyar da gwamnatinsa.
Matar da mijinta yake Gwamnan jiha irin ta Kano, jihar da ta fi kowace jiha yawan jama’a da wayewa a harkokin siyasa da karfin tattalin arziki irin na saye da sayarwa a bayan Jihar Legas, da kuma yadda aka san gwamnonin wannan zamani da jin kansu tamkar Fir’aunan zamanin Annabi Musa (AS), da su ne suke wuka suke da nama a jihohinsu sai abin da suke so ko suka ce za a yi, amma Gwamnanta ya fito bainar jama’a yana irin wadannan kalamai a kan isar matarsa.
Ke nan nunen da matar ta yi ba da wasa ko da ganganci ta yi shi ba, ka iya cewa da shawara da amincewar mijinta ta yi shi.
Don haka lokaci ne kawai zai gaskata ko haka ko akasin haka kan nunen na Gwaggo ga Kwamishinan Kananan Hukumomi Murtala Sule Garo na shi zai gaji Gwamna Ganduje a shekarar 2023, in Allah Ya kai mu.