✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood: Sunusi 442, Maryam Jankunne sun zama mashawartan Abba

Bayan Sanusi Oscar 442, Tijjani Gandu da Maryam Jankunne sun samu shiga sahun manyan masu ba wa gwamnan Kano shawara

Furodusa Sanusi Oscar 442 ya zama mai ba da shawara na musamman a kan harkokin Kannywood ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Gwamna Abba ya nada Sanuni 442 ne cikin jerin wasu mutane 42 da ya ba wa mukaman siyasa, inda wasu ’yan Kannywood suka samu shiga ciki.

Gwamna Abba ya kuma nada abokin Sanusi 442, Tijjani Hussaini Gandu a matsayin mashawarci na musamman kan harkokin nishadi.

Hakazalika ya nada tsohuwar ’yar Kannywood, Maryam Abubakar Jankunne a matsayin babbar mai ba shi shawara a bangaren matan karkara.

A kwanakin baya Gwamnan Abba ya nada na hannun daman 442, Abba El-Mustapha, a matsayin shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

Tuni dai Abba El-Mustapha ya soke lasisin ’yan Kannywood, domin rabe aya da tsakuwa a cikinsu, lamarin da ya bar baya da kura.

Sanarwar sabbin nade-naden da Sakataren Watsa Labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin ta kara da cewa Yusuf Ibrahim Sharada ya zama sabon Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Abba a fannin Fasahar Sadarwa, da Akibu Isa Murtala da ya zama Babban Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata.

Haka zalika Akibu Shehu Haske ya samu mukamin Babban Mataimaki na musamman a bangaren jaridu, da Bashir Sanata Sharada a matsayin babban mataimaki na musamman a bangaren Yada Labarai.