✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood na cike da zalinci da fasikanci – Zango

  Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A Zango ya bayyana cewa masifar da masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood take ciki ta wuce misali,…

 

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A Zango ya bayyana cewa masifar da masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood take ciki ta wuce misali, saboda zalinci da fasiqanci da riya da ‘yi don ganin ido’ da kuma cin amanar da ’yan fim suke aikatawa qarara.

 

Jarumin wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Instagram a ranar Litinin da ta gabata ya kuma ce amma daga an yi magana sai ’yan fim su ce matan cikinsu ne suke janyo wa masana’antar abin kunya.

 

Ya ce, “Wallahi matanmu ba su da laifi domin addini bai tava bai wa mace damar zama babu mai kula da ita ba. Amma a Kannywood fim xaya yarinya ko yaro za su yi sai ka ga sun buxe kamfanin kansu har ma su riqa xaukar sababbin ’yan wasa.”

 

“Wallahi, billahi daga yau ba za a qara yi mini qazafi in yi shiru ba, don kowa a cikin (kannywood) ya san kowa. Shi ya sa idan aka ce mana jahilai ba na damuwa, yanzu ni ma na gano hakan. Tun da an ce amfanin ilimi aiki da shi. Babu tone-tone domin da dama sun san inda na dosa.”

 

Jarumin ya ce don haka ’yan fim su daina jin haushin zagin da al’umma suke yi musu.

 

“Mu karvi laifukanmu, mu gyara wata qila nan gaba kaxan su yi alfahari da mu. Duk abin da na rubuta idan akwai qarya a ciki wani ya fito ya qaryata ni ko kuma a kore ni.”