✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood: Hisbah na neman jaruma Ummah Shehu

Ummah Shehu ta ce Hisbah na daukar doka ne kan talakawa.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce tana neman jarumar Kannywood, Ummah Shehu domin yi mata karin haske bisa zargin wasu jami’anta da saba wa doka.

Babban Kwamandan hukumar, Harun Sani Ibn Sina ne ya shaida wa manema labarai hakan ranar Talata a birnin Dabo.

Ibn Sina ya ce hukumar ta baza komarta domin cafke jarumar da take nema ruwa a jallo.

Bayanai sun ce jarumar ta zargi Hukumar Hisbah da kin daukar doka a kan masu idanu da kwalli sai iya marasa galihu.

Cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram, Umma ta caccaki Hukumar Hisbah game da kama wata jaruma a Kannywood, Sadiya Haruna da laifin yada hotuna da bidiyon batsa a dandalan sada zumunta.

Ummah Shehu ta fusata matuka kan matakin da Hisbah ta dauka inda ta yi zargin cewa hukumar ta fi mayar da hankali wajen hukunta talakawa da ‘yan fim bayan kuwa masu hannu da shuni da kuma jami’an hukumar suna tafka ta’asa ba tare da an dauki mataki a kansu ba.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Ummah Shehu game da lamarin, amma jarumar ba ta amsar waya da sakon da wakilinmu ya tura mat aba ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Tuni dai wata kotun musulunci a ranar Litinin, a Jihar Kano ta yanke wa jaruma Sadiya Haruna hukuncin koma wa makarantar Islamiyya, bayan da ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi.