✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kande mai wasa da ruwa’

Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fata ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Kande mai wasa a ruwan sama’. Labarin…

Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fata ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Kande mai wasa a ruwan sama’. Labarin ya yi nuni ne ga illar wasa a ruwan sama. A sha karatu lafiya.

Kande yarinya ce mai son wasa da ruwa koda ba ruwan sama ba. Saboda yawan wasa da ruwa, a kullum sai ta canza kaya akalla sau uku. 

Mahaifiyarta a kullum sai ta yi mata fada, amma Kande ta ki daina wannan hali na yawan wasa da ruwa.

Rannan sai hadari ya hadu sosai aka fara ruwan sama Kande ta saci jiki ta fita, ti shiga ruwan saman nan ya yi mata duk ta jige sharaf. 

Tana isa gida sai ta shiga yin kakkarwar sanyi.  Duk da kayan da ta canza na jikinta, ba ta daina jin sanyin ba.  Sai ta shiga bargo ta rufe kanta ban da tari babu abin da take yi hade da karkarwa. A hakan mahaifiyarta ta same ta. Koda ta taba jikinta sai ta ji jikin ya yi zafi. A haka suka kwana idonsu biyu sai washegari aka kaita asibiti.

Likita ya kwantar da su, kuma aka rika yi mata allurai da ba ta magunguna.  Da kyar da jibin goshi ta samu lafiya, tun daga ranar Kande ta daina yin wasa da ruwa.

Tare da fatan Manyan gobe za su kasance masu ladabi da biyayya ga iyayensu.