Masallacin NASFAT na kasa da ke Abuja
Fassarar Salihu Makera
Huduba ta Farko:
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa muna neman taimakonSa, muna neman shiriyarSa, kuma muna neman tsarinSa daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, kuma Wabda Ya batar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, Wanda Yake cewa: “Suna tambayarka game da Sa’a (Alkiyama), wai yaushe ne matabbatarta? Me ya hada ka da ambatonta? Zuwa ga Ubangijinka karshen al’amarinta yake. Kai mai gargadi kawai ne ga mai tsoronta. Kuma kamar su, a ranar da za su gan ta, ba su zauna ba face a lokacin maraice ko hantsinsa.” Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, wanda yake cewa: “Sa’a ba za ta tsaya ba, sai wasu kabilu daga al’ummata sun riski (koma) mushirikai kuma sai sun bauta wa gumaka.” Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da amintarwa.
Bayan haka, bayin Allah, ku bi Allah da takawa, ku sani Ubangijinku Yana yi muku wasiyya da cewa: “Kuma wanda ya bi Allah da takawa, Allah zai sanya masa mafita” kuma Ya ce: “Kuma zai sanya masa wani sauki daga al’amarinsa.” Allah Ya sanya ni da kuma ku cikin bayinSa masu takawa.
Hudubarmu ta yau insha Allahu za ta yi magana ce a ka kananan Alamomin Sa’a.
Lallai yana daga cikin cikakkiyar hikimar Allah da Ya boye wa bayinSa lokacin tashin Alkiyama, babu wani daga cikin halitta da zai iya riskar haka, ya alla daga cikin mala’iku makusanta ne ko daga cikin annabawa da manzanni. Allah Madaukaki Ya ce: “Suna tambayarka game da Sa’a yaushe ne matabbatarta? Ka ce, abin sani iliminta yana wurin Ubangijina ne, babu wanda ya san lokacinta face Shi, (sanin haka) ya yi nauyi a cikin sammai da kasa, ba ta zuwa muku face a afke. Suna tambayarka kamar kai mai tsarewa (sani) a kanta. Ka ce: “Abin sani iyaka iliminta yana wurin Allah, amma mafi yawan mutane ba su sani.” Kuma Allah Madaukaki Ya sake cewa: “Mutane suna tambayarka game da Sa’a, ka ce iliminta yana wurin Allah, kuma me ya sanar da kai, la’alla Sa’a ta kasance a kusa?”
Mala’ika Jibrilu ya tambayi Annabi (SAW) game da Sa’a, sai ya ce, wanda aka tambaya bai fi mai tambayar sanin komai ba game da ita. Wadannan biyu, mafi girma cikin mala’iku da mafi girman ’ya’yan Adam, ba su san yaushe Sa’a za ta tsaya ba, to yaya lamarin zai kasance ga waninsu daga cikin halittu?
Amma daga cikin rahamar Allah, sai Ya sanya wasu alamomin Sa’a da suke nuni ga karatowarta da kusancinta ta yadda mutane za su yi tattali domin haduwa da Allah suna da imani sahihi da kyawawan ayyuka, kuma wannan shi ne guzurin gidan Lahira wanda babu wani guzuri bayansa. Allah Madaukaki Ya ce: “Shin suna jira ne face Sa’a ta zo musu afke, to hakika alamunta sun zo musu, kuma lamari zai kasance da su, idan tambatonsu ya zo musu?”
Na farko daga alamoin Sa’a, shi ne aiko Annabi (SAW). Hakika ya tabbata daga gare shi (SAW) maganarsa cewa: “An aiko ne ni da Sa’a kamar wadannan biyu, sai ya nuna manuniyarsa da yatsarsa ta tsakiya.” Buhari ya ruwaito.
Kuma daga cikin alamun Sa’a akwai tsagewar wata a zamaninsa (SAW). Allah Madaukaki Ya ce: “Sa’a ta kusanto. Wata ya tsage.” An karbo daga Anas (RA) ya ce: “Lallai mutanen Makka sun tambayi Manzon Allah (SAW) kan ya nuna musu wata aya, sai ya nuna musu tsagewar wata.
Kuma daga alamomin Sa’a akwai bayyanar bautar gumaka a cikin mutane da yawa na al’ummar Musulmi da yin ridda suna komawa ga kafirci. Buhari ya ce a cikin sashinsa daga Abu Huraira (RA) cewa “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Sa’a ba za ta tsaya ba sai mata sun doka dausi a kan zul-khilsah. Ya ce, zul-khilsah dagiyah wani gunki ne da suke bauta masa a zamanin Jahiliyya. Annabi (SAW) ya ce: “Sa’a ba za ta tsaya ba, sai wasu kabilu daga al’ummata sun riski mushirikai kuma sai sun bauta wa gumaka. Kuma lallai wasu makaryata daga cikin al’ummata talatin dukansu kowannensu zai rika zaton shi annabi ne, to ni ne cikamakin annabawa babu wani annabi a bayana.” Abu Dauda da Tirmizi suka ruwaito.
Kuma yana daga cikin alamomin Sa’a har wa yau, akwai bayyanar tabarruji da yawace-yawancen mata gaskatawa ga fadinsa (SAW) kan daya daga cikin nau’o’in mutanen da bai gan su ba a rayuwarsa da mata masu yawo tsirara masu karkata kawunansu kamar kawunan rakuma ba za su shiga Aljanna ba, ko kanshinta ba za su ji ba, kuma ana jin kanshinta daga tafiyar kaza da kaza.” Muslim ya ruwaito.
Kuma daga cikin alamomin Sa’a akwai gushewar duwatsu daga muhallansu da yawan girgizar kasa da yawaitar cututtukan da mutane ba su san su a baya ba da yawaitar dujal-dujal da masu miyagun huduba, kuma hakika duk wadannan sun faru. Kuma daga ciki akwai canjawar yanayi, ana cikin lokacin hunturu sai a hadu da yanayin lokacin bazara (a surka zafi), lokacin bazara kuma sai a hadu da yanayin hunturu (a surka sanyi). Haka akwai karancin ilimi da yawaitar jahilci, ma’ana jahilitar addini. Muna neman tsarin Allah daga fitintunun da suke suke raunana zukata da imani. Allah Ya yi mana albarka a cikin Alkur’ani Mai girma.
Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Muna gode masa a bisa kyautatawarsa, muna yi maSa shukura a bisa datarwarSa da rahamarSa gare mu. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, kuma na shaida cewa lallai Shugabanmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ina yi muku wasiyya da ni kaina da bin Allah Madaukaki da takawa, domin a cikin hakan akwai alherin duniya da Lahira baki daya.
Ya bayin Allah! Daga cikin alamomin Sa’a akwai yawaitar kashe-kashe. An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: Annabi (SAW) ya ce: “Sa’a ba za ta tsaya ba, har sai harju ya yawaita.” Sai sahabbai suka ce: “Mene ne harju ya Manzon Allah!” Ya ce: “Kisa, kisa!” Kuma daga gare shi (RA), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Na rantse da Wanda raina yake hannunSa, duniya ba za ta tafi ba, sai wata rana ta zo wa mutane da wanda ya yi kisa bai san a kan wane dalili ya yi kisan ba, haka wanda aka kashe bai san a kan me aka kashe shi ba.” Muslim ya ruwaito.
Lallai wadannan fitintunu ukubobi ne daga Allah Yana sallada su a kan wanda Ya so a lokacin da suka saba wa umarninSa suka kafirce ko suka butulce wa ni’imominSa, sai Ya dandana musu tubar yunwa da tsoro saboda abin da suka kasance suna aikatawa.
Mu da muke tare a nan, muna tunatar da kawunanmu da kuma ku kan wajibcin bin Allah da takawa da kiyayen abin da Ya ni’imta a kanmu na daga ni’imomin da ba su kidayuwa kuma ba su da iyaka. Daga cikinsu akwai ni’imar zaman lafiya.
Muna rokon Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya.
“Lallai ne Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta hakkinsa, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da kuma zalunci. Yana yi muku wa’azi tsammaninku kuna tunawa.”
Imam Sharafudeen Abdussalam Aliagan shi ne Babban Limamin Masallaicn NASFAT na kasa da ke Abuja, kuma za a iya samunsa ta tarho mai lamba: 080347108620