Salam Editan Aminya. Ko shakka babu galibin ‘yan Majalisun Tarayyan Najeriya guguwar Shugaba Muhammadu Buhari suka bi, ba su cancanta ba, shi ya sa tun yanzu suka fara juya masa baya wajen zaben Shugaban majalisun dattawa da na wakilai.
Gargadi ga ‘yan majalisa
Assalamu alaikum Aminiya, don Allah ku mika mini wannan gargadi ga ‘yan majalisunmu na yankin Arewa-maso-Gabas. Hakika sun nuna mana dama ga duniya halayyarsu na son mulki a zahiri har suka mance da galabaitacciyar yankinsu da take matukar bukatar gudumawarsu. Sai dai kash. Sun barar da wata dama da muka samu saboda yadda wasu suka yi biris da umarnin jam’iyya, bayan an siye su da cewa za a ba su mukamai. Yayin da jam’iyyar PDP ta shammacesu ta musu wankin babban bargo, inda suka ki marawa nasu baya, suka kuma rasa nasu bukatun. Wannan ya isa ya zama darasi gareku idan har kuna da kishin al’ummar ku, Sannan muna fatan wannan ya kasance na karshe da zaku mana wannan babbar tabargaza ta rashin samun mukamin shugaban majalisar dattawa. Daga karshe nake addu’ar Allah Ya sa hakan shi ne ma fi alheri, su kuwa da Allah ya zaba, Allah Ya ba su ikon gudanar da jagoranci cikin gaskiya da rikon amana.
Daga Sakatare Usman Bin-Affan , Jihar Yobe, 08038001563
Yakamata a yi dokar ci gaban jama’a
Sababbin ’yan majalisa na jihohi da na tarayya.Yaka mata ku mayar da
hankali wajen samar da dokokin da za su amfani al’umma. Domin ci gaban
al’ummar da kasa baki daya.
Daga Haruna Muhammad Katsina
Sako ga Shugaba Buhari
Salam Edita, don Allah ka isar mini da sakona ga sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya yi daidai da ya sa aka mayar da cibiyar rundunar sojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram zuwa garin Maiduguri.
Daga Hussaini Mikah Rijau, Jihar Neja
Dokar daurin rai-da-rai ga masu aikata laifin fyade
Salam Aminiya, shakka babu daukacin ’yan Najeriya sun yi na’am da dokar daurin rai-da-rai ga masu aikata laifin fyade, da fatan zamu gani a kasa. Allah Ya shiryesu.
Daga dahiru Dauda (KGY) Bindawa
daurin rai-da-rai ga masu fyade ya yi daidai
Zuwa ga ’Yan Majalisar Tarayya. Hukuncin daurin rai-da-rai ga masu fyade ya yi daidai, amma wane hukunci kuka tanadarwa maza da mata masu yin shiga mai nuna tsiraici? Domin kasha 75 cikin 100 na fyaden da ke faruwa, yana faruwa ne ta sanadiyyar sanya tufafi masu nuna tsiraici.
Daga Bashiru Mai Katako, Sakkwato
Kira ga Shugaba Buhari
Salam Edita, ina jadda godiyata agareku saboda dama da kuke bamu ta isar da sakonninmu. Da farko zan fara ne da godiya ga Allah da Ya azurtamu da adalin shugaba, Alhamdulillah. Na biyu shawarata ga Shugaba Muhammadu Buhari ita ce, don Allah ya kawo mana dauki cikin harkar tuki saboda ni direba ne a babban garejin unguwar Jabi da ke Abuja. Idan aka duba babban garejin Jihar Adamawa da na Jihar Sakkwato sun fi na Abujan kyau. Sannan a duba mana harkar aikace-aikacen jami’an b.I.O da ’yan sitika. Don Allah shugaban kasa ka mayar da wadannan takardu guda-guda koda kuwa kudinsu zai fi wadancan.
Daga Sabo Jabi, Abuja, 08187808136
A koma gona
Assalamu Alaikum Editan. Tabbas idan gwamnatin Najeriya tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi za su samar matasan kasar nan da takin zamani da wasu kayan ayyukan noma to lallai mu matasa zamu rugunmi harkar noma gadan-gadan. Ganin cewa harkar noma tafara ja baya musamman a yankin Arewaci bisa haka ne muke kira ga Shugaba Muhammadu Buhari akan ya mayar da hankali akan harkar noma tare da farfado da masana’antun kasar nan wadanda suka durkushe sanadiyyar rashin samun wadatacciyar wutar lantarki.
Daga karshe muna addu’ar Allah Ya bai wa shi ikon sauke nauyin alkawurraan da ya yi wa ‘yan Najeriya.
Daga Kwamared Nura Bello, Jihar Zamfara, 08032558025.
Yabo ga Aminiya
Salam Edita, ina son ka ba ni dama na yi maku godiya kan namijin kokari kan gagarumar gudunmuwa da kuke bayarwa musamman kan harkokin zabe da siyasa, kuma abin a yaba muku ne, Allah Ya kara basira.
Daga Mustapha Muhammad, Kasuwar Panteka, Kaduna.
Taya Sarkin Kano murna
Salam Edita, don Allah ka ba ni dama na taya mai marbata Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II munar cika shekara daya kan karagar milkin masarautar Kano mai tarihi. Muna addu’a Allah kara wa sarki lafiya. Har ila yau, ina mika ta’aziyata ga masaratar ta Kano kan cika shekara daya da rasuwar Mai Martaba Alhaji Ado Bayero Allah Ya jikansa da rahma ya kyautata makwancinsa.
Daga Muhammad Ahmad Idris, Kabuga Kano, 08031818318
Salam Edita, ina taya Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II murnar cika shekara guda akan gadon sarauta.
Daga Aliyu Abubakar Harbo