✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kamfanonin waya za su yanke hulda da bankuna saboda taurin bashi

Kamfanonin sun ce bankuna na cire kudin kwastomomi, amma su hana su hakkinsu

Kamfanonin sadarwa sun yi barazanar yanke hulda da bankunan Najeriya da kuma sauran kamfanonin hada-hadar kudi saboda taurin bashi.

Barazanar daukar wannan mataki ya fito ne daga Shugaban Kungiyar Kamfanonin Sadarwa ta Najeriya (ALTON), Injiniya Gbenga Adebayo, a wani jawabi da ya yi a taron kungiyar masu bayar da rahotanin kan al’amuran sadarwa ta kasa (NITRA) a jihar Lagos.

Injinya Adebayo ya ce bankuna suna cire kudinsu daga kwastomininsu amma sai su ki biyan kamfanonin sadarwa nasu hakkin.

“Haka ba za ta yiwu ba, domin banki ba zai bi ka bashin kwabo ba ya kuma bar ka ka sarara, sai ka biya, amma yanzu mu yanzu ga shi muna bin su bashi amma sun ki biya,” inji Adebayo.

Sannan ya ce, idan suka yanke huldarsu da bankunan, mutane ba za su iya aikewa da kudi ko karbarsu ba ta hanyoyin zamani kamar waya da suransu.

Adebayo ya kuma ce an kusa kai wa ga hakan, domin kamfanonin sadarwar ba su da zabi idan bankunan su ka ci gaba da kin biyan bashi face su dauki matakin.