✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanonin hada motoci 52 sun durkushe a Najeriya

Dalilan da kamfanonin hada motoci 52 daga cikin 58 suka daina aiki a shekara 7 a Najeriya

52 daga cikin kamfanonin hada motoci 58 da ke aiki a Najeriya sun daina aiki daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

A shekearar 2015 ne Gwamnatin Tarayya ta bai wa kamfanoni 58 salilin hadawa da kera motoci a karkashin shirin samar da motoci a cikin gida (NADDC).

Aminiya ta gano masu zuba jari sun sanya sama da Dala biliyan daya a karkashin shirin, wanda zai fara da shigo da sassan da kuma kayan motoci (SKD) domin hadawa a cikin gida kafin daga bisani a fara kerawa (CKD) a Najeriya.

Amma Mataimkin Manajan Daraktan Kamfanin Motoci na CFAO, Kunle Jaiyesinmi, ya ce kawo yanzu shida daga cikin kamfanoni 58 din ne suke aiki, sauran sun rufe.

Jaiyesinmi ya ce hakan ya haifar da damuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki game da makomar masana’antar motoci a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a wurin taron horon ’yan jarida masu daukar rahoto a bangaren motoci karo na bakwai a Legas.

Matsalar watsi da Kudirin NAIDP

Jaiyesinmi ya bayyana rashin sanya hannun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan Kudurin Dokar Bunkasa Bangaren Motoci Na Kasa (NAIDP Bill) wanda Gwamantin Goodluck Jonathan ta yi ya kawo wa bangaren cikas. 

A cewarsa, hakan ne ya sa yawanin masana’antun suka rufe — su kansu CFAO sun mayar da ma’aikatansu na mai aikin hada motoci sun koma aikin kanikanci.

Ya ce, “Lokacin da NADDC ya fito da tsarin, an faro shi ne mataki-mataki; SKD1 da SKD2 sannan SKD3.

“An yi zaton cikin shekara biyar za a kai matakanin kera motoci; ya kamata a 2024 mu fara kerewa, amma yanzu 2022 amma ba mu wuce yin SKD ba.

Matsalolin masana’antar motoci a Najeriya

“Dole mu ci gaba da yin SKD ne saboda ba zai yiwu a yi batun CKD ba alhali masana’antar tama da masu samar da sauran kayan da muke bukata ba sa aiki.

Ya ce sauran matsalolin su hada da karancin samun canjin Dala domin shigo da injinan aiki daga kasashen waje da kuma yawan kara harajin da hukumar Kwastam ke yi kan motocin da ake shigo da su daga kasashen waje.

Sauran sun hada da tafiyar hawainiya wajen tantance kwantainonin kayan da aka shigo da su Najeriya daga kasashen waje da suran matsaloli.

Ya bayyana cewa, “Yanzu shigo da motoci daga kasashen waje ya fi hada su a Najeriya arha, shi ya sa kamfanoni shid ne kawai suka rage masu hada motoci a Najeriya.