✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanoni dubu 800 ba sa biyan haraji – Ministar Kudi

A daidai lokacin da wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ke bin matakan rage dogaro da arzikin fetir, Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta bayyana cewa ma’aikatar…

A daidai lokacin da wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ke bin matakan rage dogaro da arzikin fetir, Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta bayyana cewa ma’aikatar tata ta gano kimanin kamfanoni dubu 800 da ba su taba biyan haraji ba, wadanda suka hada da na ‘yan kwangila.

A wata takarda da ministar ta rubuta, kuma aka raba ta ga manema labarai kan hanyoyin bunkasa tattalin arzikin Najeriya, ta ce yanzu haka gwamnati na bincike a kan kamfanonin. Sai dai kuma ba a bayyana sunayen kamfanonin ba, da kuma irin ayyukan da suke yi a kasar ba.

Ministar ta kara da cewa gwamnati ta fi samun kudaden haraji daga albashin ma’aikata, wato kusan kashi 95 daga cikin miliyan 14 da ya kamata su biya haraji, inda ta ce a shekarar 2016 mutane 241 ne kacal suka biya haraji wadda ya kai Naira miliyan 20.

“Arzikin man fetir da Najeriya ke tinkaho da shi ne musabbabin da ya sa gwamnatocin da suka shude suka yi sake wajen karfafa gwiwar wasu hanyoyin samun kudaden shiga. Amma a yanzu ma’aikatar kudi ta kaddamar da wani shiri na tattaro bayanai daga ofisoshin gwamnati da bankuna da hukumar kwastam da kuma wadanda suka mallaki kamfanonin kansu.

Koda yake wasu bayanai daga hukumar karbar haraji ta kasa na nuni da cewa babban kalubalen da hukumar ta fi fuskanta shi ne gano hakikanin inda kamfanonin su ke aiwatar da ayyukan nasu, duk kuwa da cewa suna da rijistar gwamnati. Haka kuma bayanan na cewa wannnan adadi da ministar ta fadi ba shi ne yawan jadawalin kamfanonin da ba su biyan harajin ba, domin a Ikoyi na Jihar Lagos kawai akwai kamfanoni sama da dubu takwas da aka gano cewa ba su taba biyan haraji ba. Haka kuma hukumar ta zargi lauyoyi wajen taimaka wa kamfanonin kaucewa biyan haraji, inda suke masu rijista ba tare da sun tantance adireshin da kamfanonin suke ba, da kuma manufar kafa kamfanin, lamarin da ke bai wa jami’an hukumar karbar harajin matukar wahala.

Bugu da kari kuma, wasu rahotanni dake kunshe cikin takardun ‘Paradise Papers’ sun Ambato wasu manyan attajirai da ‘ya siyasa wadanda bas u biyan haraji ciki kuwa har da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki.

Sanata Sarakin, wanda shi ne mutum na uku mafi girman mukami a tsarin siyasar Najeriya, a matsayin wanda ya kafa kamfanin Tenia Limited a tsibirin Cayman Islands a shekarar 2001, kuma ya ci gaba da zama daraktan kamfanin da kuma mamallakinsa har zuwa shekarar 2015. 

Koda yake Shugaban Majalisar Dattawan ya karyata zargin na kin biyan haraji da ake masa a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Yusuph Olaniyonu ya aikewa manema labarai, ya kuma bayyana matsayin wani kamfaninsa da aka kwarmato cewa ya bude shi ne domin kaucewa biyan haraji. Inda sanarwar ta danganta lamarin da siyasa domin bata sunan Sanata Saraki. Ya na mai cewa mai gidansa bai saba doka ba kuma bude kamfanin bai saba wa ka’ida ba. “An kafa kamfanin a shekarar 2001 tun lokacin da Saraki bai ma shiga siyasa ba, sannan kamfanin bai taba aiki ba tun da aka kafa shi, bai taba mallakar wata kadara ba, bai yi ciniki ko kuma wani kasuwanci ba, kuma ba shi da wani asusu a wani banki,” a cewa Mista Olaniyu.