✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Yahoo zai rage ma’aikatansa

A shekaranjiya Laraba ne Kamfanin Intanet na Yahoo ya bayyana cewa zai rage kashi 15 bisa 100 na ma’aikatansa, bayan asarar da ya tafka ta…

A shekaranjiya Laraba ne Kamfanin Intanet na Yahoo ya bayyana cewa zai rage kashi 15 bisa 100 na ma’aikatansa, bayan asarar da ya tafka ta kusan Dala biliyan hudu da rabi.
Kamfanin wanda shi ne na farko a harkar intanet a cikin shekara ta 1990, ya sha rasa tallace-tallace ga abokan karawar kasuwancinsa wato Google da kuma Facebook.
Yahoo ya kuma ce zai rufe biyar daga cikin ofisoshinsa, kana zai sayar da wasu kadarorinsa, kamar yadda BBC ta bayyana.
Jagorar kamfanin, Marissa Meyer, ta ce rage girman kamfanin zai sa ya kasance mai alkibla, sanan zai gyara makomarsa wajen inganta kasuwancinsa.