✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin NNPC da tsarin Jari-Hujja a Najeriya

Tun lokacin da masu neman shugabancin Najeriya suka fara kamfen, ba bayyana manufa suke yi ba, burinsu a dauko mutane haya (Naira 500 da hula…

Tun lokacin da masu neman shugabancin Najeriya suka fara kamfen, ba bayyana manufa suke yi ba, burinsu a dauko mutane haya (Naira 500 da hula ko riga), a cika filin wasa, a yi ta cin mutuncin juna da yada karairayi.

Koda muhawarar ’yan takara da aka yi ba ta yi armashi ba.

Daya daga cikin abubuwan da zan iya cewa talaka ya mai da hankali a kansa shi ne, batun dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar zai sayar da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC).

Tambaya a nan, ita ce, PDP za ta sayar da NNPC, shin wannan na nufin APC ta yi alkawarin ba za ta sayar da NNPC ba ne? ’Yan Najeriya na bukatar sanin matsayar kowace jam’iyya a kan wannan batu. Da yawa za su zabi PDP saboda akidarsu ta Jari-Hujja ciki har da sayar da NNPC, da yawa za su ki zaben PDP saboda batun sayar da NNPC. To amma dole kowace jam’iyya ko dan takara ya fito a hukumance ya gaya mana mene ne matsayinsu game da sayar da NNPC, dama sayar da kadarorin gwamnati. Wannan shi zai ba talaka dama, duk wanda Allah Ya ba mulki, a rike shi bisa hujja.Dole talakan Najeriya ya nuna ya san kansa ta yadda banzaye ba za su yi wasa da hankalinsa ba.

Akasarin talakawan Najeriya ba su da masaniya kan yadda NNPC ke tafiya, kuma ba su da masaniya game da gudanarwa ko dokokin da suka samar da kamfanin. Don haka yana da wuya mutum ya bayyana sahihin ra’ayi kan NNPC ko masana’antar mai. MIsali, talaka nawa zai iya ba da amsa cewa NNPC mallakar gwamnati ne baki daya, ko akwai hannun jari daga kamfanonin cikin gida da na waje? Sannan nawa NNPC ke samarwa duk rana nawa kuma yake zubawa a Asusun Tarayya?

Sannan yunkuri nawa aka yi lokuta daban-daban domin a gyara NNPC, sannan wane matsayi dokar gyara bangaren mai (PIB) da ke gaban majalisa take ciki yanzu haka? Wa ya isa yanzu ya gaya mana da hujja ko nawa NNPC ya samar daga 2015 zuwa yau? Na tabbata ko Shugaba Muhammadu Buhari bai da wannan bayani.

Na ji dadi yadda talakawa da yawa suka nuna kyamar akidar sayar da kaddarorin gwamnati, kuma duk wanda Allah Ya ba mulkin ,za mu duba mu ga ko talakawa za mu iya dagewa a kan kyamar sayar da kadarorin gwamnati, ba ma NNPC kawai ba!

Daga karshe, na lura kamar Jam’iyyar APC ba ta goyon bayan sayar da kadarorin gwamnati, to muna fatan idan ta sake kafa gwamnati za ta rusa Hukumar BPE, sannan duk wani tsari na sayar da kadarorin gwamnati ciki har da layin dogo da komai duk a hana.

Na so a ce gwamnati ta yi amfani da yakin kamfen ta gaya mana daga 2015 zuwa yanzu nawa ta samu daga NNPC?

Sannan rahoton NEITI na shekarar 2017 da ya nuna NNPC ya ki saka kudi sama da Naira tiriliyan 7 a lalitar gwamnati, gaskiya ne ko karya?

Daga Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina

Babban Sakataren Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa 08165270879