Kamfanin Man Fetur na NNPC ya bayyana garambawul din da ya yi inda kamfanin ya yi sabbin nade-nade tare da sauya wa wasu manyan jami’an kamfanin wurin aiki.
Shugaban Kamfanin, Dokta Maikanti Baru ya fada wa ma’aikatan kamfanin cewa sabbin nade-naden da kamfanin ya yi zai taimaka wa kamfanin tunkarar kalubalen da ke gabansa sannan kuma zai taimaka wajen cike gibin da aka samu sakamakon ritayar da wasu ma’aikatan kamfanin suka yi.
Ya bayyana cewa jami’ai 55 na kamfanin lamarin ya shafa inda aka mayar da Tsohon Shugaban Bangaren Kididdiga, Roland Ewubare zuwa Bangaren Saka Hannun Jari a matsayin babban Janar Manaja sannan Babban Mai taimaka wa Shugaban Kamfanin NNPC, Diepriye Tariah, ya karbi aiki daga wurin Tsohon Shugaban Bangaren Kididdiga Ewubare.