✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kamfanin ‘Facebook’ na shirin sallamar ma’aikata 11,000

Wannan dai shi en irinsa mafi girma tun bayan kafa kamfanin a 2004

Kamfanin Meta, mallaka shafukan Facebook da WhatsApp da Instagram ya ce zai sallami kashi 13 cikin 100, kwatankwacin sama da mutum 11,000 daga aiki cikin wannan shekarar.

Idan sallamar ta tabbata, hakan zai zama irinsa mafi girma da ya taba aukuwa a tarihin kamfanin tun bayan kafuwarsa shekara 18 da suka gataba.

Kamfanin ya ce ya shirya daukar wannan mataki ne saboda tsadar gudanar da harkokinsa da yake fama da ita, hadi da rashin samun tallace-tallacen da za su kawo masa kudi.

Kazalika, kamfanin na Meta ya ce, sallamar dubban ma’aikatansu da wasu manyan kamfanonin fasaha irin su Twitter da Microsoft suka yi, na daga cikin dalilan da suka sa shi ma zai rage yawan ma’aikatan nasa.

Ya kara da cewa annobar tsadar kayayyaki da kudin ruwan da ake jibga musu, sun yi silar fadawar kamfanoni cikin mawuyacin hali.