Sama da ma’aikata dubu daya ne kamfanin Al-Dusar mallakar dan kishin kasa Alhaji Muhammadu Usman Sarki ya bayar da bashin kayan girki na zamani masu amfani da iskar gas a Jihar Katsina.
Bikin bayar da wadannan kayan bashin ga ma’aikatan an yi shi ne a harabar kamfanin da ke cikin garin Katsina a ranar Talatar da ta gabata, bayan kulla yarjejeniya a tsakanin kamfanin da kungiyar kwadago ta jihar bisa amincewar gwamnatin jihar.
Kamar yadda Babban Sakataren ofishin Shugaban ma’aikata na jahar Alhaji Idris Tune, Alhaji Lawal Ado ya ce,”wannan yunkuri na wannan kamfani yazo daidai lokacin da ake bukatarsa, domin gwamnati ta dade tana tunani akan yadda zata rage gurbatar muhalli, saran itatuwa da kwararowar hamada gami da zaizayar kasa na barazana ga jahar wanda samar da wadannan kayan girki da wannan kamfani ya yi zasu kawo sauki mutuka ta fuskar wancan kalubale.
A jawabin Shugaban Kamfanin Al-Dusar Alhaji Muhammadu Usman Sarki ya ce, ya dade yana tunanin irin gudunmuwar da zasu bayar domin ganin cewa, an yaki dabi’ar saran itatuwa gami da yin girki da kalanzir wanda ya ce babban hadari ne ga muhalli ga kuma tsada.
“Yin amfani da hanyar zamani a wajen sanwa ko girki musamman ta amfani da tukunya da murhun zamani masu aiki da iskar ‘Gas’ zai kawo raguwar gurbatar muhalli, sannan kuma zai kawo saukin saran itatuwa da ake barkatai wanda hakan ba karamar illa bace ga tattalin arziki da kuma lalacewar muhallanmu bayan kara ba hamada damar shigo wa ga kuma zaizayar kasa domin ba bu itatuwan dake zama kariya akan haka”. Kamar yadda ya ce, bisa lura da wadancan abubuwa ne yasa kamfanin ya kulla yarjejeniya da kungiyar kwadago ta jahar bayan amincewar Gwamnatin jahar karkashin jagorancin Gwamna Masari suka samar da wadannan kayan girki isassu domin raba wa ma’aikatan jahar bashi a cikin sassaukan farashin da zasu iya biya a cikin watanni uku.
Ita kuwa kungiyar kwadago ta jahar wanda Sakataren kungiyar na jaha Alhaji Abdullahi Balange ya wakilta, ya jinjina wa wannan kamfani akan bullo da wannan hikima wadda ya ce ita ce, ta farko da aka taba yi a jahar. Kungiyar ta ce, ma’aikatan jahar ba zasu yi kasa a gwiwa ba ta wajen biyan wannan bashi wanda ya ce, mai kama da tukuici.
“Wannan kamfani ba wai ma’aikatan da ke aikin gwamnati a halin yanzu kadai ya taimaka wa ba, hatta da wadanda ba su da aikin yi yanzu wannan kamfani ya samar masu da ayyukan yi.”
Da Aminiya ta tuntubi wasu daga cikin wadanda suka amfana da wannan bashi, sun nuna farin cikinsu a kan irin yadda za su samu saukin kashe kudadensu a wajen sayen kayan girki.