Wani hoton bidiyo daga kasar China ya dauki hankalin masu bibiyar shafukan sada zumunta na zamani bayan nuna wani rago jinsin llama-alpaca mai shekara biyu a cikin ofishin wani kamfani.
A yayin da wasu kamfanoni suke kai dabbobi cikin ofishinsu don nishadantar da ma’aikatansu lokacin da suka yi aiki suka gaji don warware gajiyarsu, mafi yawan lokuta an fi kai mage da kananan karnuka ne.
Amma a wannan karon wani kamfani a yankin Wudi na kasar China ya dauki hayar wani rago mai suna Tuo Baiwan, jinsin llama-alpaca ya rika yawo a cikin ofishin don nishadantar da ma’aikata.
Ragon dai tsayin gashinsa yana da ban sha’awa kuma Rago Tuo yana da matukar son jama’a su kula shi, sannan jama’a na son yin hulda da shi.
Babban dalilin kamfanin na daukar hayar ragon shi ne nishadantar da ma’aikata idan suka gaji da lokacin da suke tsakiyar aiki, sannan su kasance cikin farin ciki yayin gudanar da aikinsu.
A cewar ma’aikatan kamfanin, ragon na faranta masu rai kullum sannan yana ba su kariya.
Manajan Kamfanin, Mista Gao Tong ya bayyana wa kafar talabijin ta Ruptly TB cewa, “Duk da yake ragon matashi ne saboda shekararsa biyu ne kacal amma muna sonsa matuka.”
Idan ragon bai kewayawa a tsakanin ma’aikata a cikin ofishin kamfanin ba, yakan fita harabar kamfanin don yin kiwo.
Kamfanin Chinan ya fara daukar kananan bidiyon ne lokacin da ragon ke kewayawa a tsakanin ma’aikatan da ke cikin ofishin tare da nishadantar da sauran ma’aikatan, hakan ya sa ragon shahara a manhajar Douyin wanda aka fi sani a duniyar yanar gizo ta TikTok.
Ma’aikatan sun ce, ba za su iya tantance takamaimen aikin ragon a kamfanin ba, sai dai kawai a iya kiransa da Jami’in Nishadantar da Ma’aikata.