✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamen da ake yi a Legas ne yake damuna -Abdullahi Maigyaran Risho

Wani bawan Allah mai suna Abdullahi Usman da ke yin sana’ar gyaran risho da kera rariya a Legas, ya ce tsarin da gwamnatin Jihar Legas…

Wani bawan Allah mai suna Abdullahi Usman da ke yin sana’ar gyaran risho da kera rariya a Legas, ya ce tsarin da gwamnatin Jihar Legas ta bullo da shi na kama masu tallace-tallace a kan titunan jihar ce matsalar da ke ci masa tuwo a kwarya.
Malama Abdullahi dan kimanin shekaru 51, ya yi furucin hakan ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a wurin da yake sana’arsa a unguwar Bagulori, a karshen makon da ya gabata.
Ya ce, “Komai yana tafiya daidai dangane da sana’ata, amma babbar matsalar da take damuna ita ce ta kamen da jami’an tsaftace muhalli na Jihar Legas ke mana idan muka yi talla a titi. Da gwamnati za ta daina kama mu da mun ji dadi. Wani lokaci idan suka kama ka, sai su ce sai ka biya tara. Idan kuwa ba ka yi sa’a ba sai su kai ka kurkuku. Wannan shi ne abin da yake damuna”.
Ya cigaba da cewa, “Da a ce ba a kame a Legas da kuwa mun sami alheri sosai fiye da yadda muke samu a yanzu. Yanzu saboda kama mu da ake yi, sai dai mu zauna wuri daya muna yin sana’a. Ka ga an sanya mu cikin takura da matsatsi. Muna rokon gwamnatin Legas ta sakar mana mara, ta kyale mu nemi halas dinmu. Ba sata muke yi ba, guminmu muke nema, ya kamata gwamnati ta taimaka mana mu sami abincin da za mu ci da iyalanmu”.
Abdullahi, wanda yake da mata biyu da ’ya’yan shida, ya bayyana cewa ya shafe shekaru kimanin 30 yana sana’ar kerawa da gyara risho da rariyar tankade.
Ya kara da cewa ko da kamfanoni masu zaman kansu suna amfana da kere-keren da suke yi.
Ya bayyana cewa banda kera rariya da injin risho yana gyaran manya da kananan tukwane.
Ya ce ya koya wa yara kimanin 16 sana’ar kuma tuni suka bude shagunansu na kere-kere.
Dangane da kayan sarrafawa ya nuna yana amfani da guduma da wuka da kuma almakashi.