Kasar Kamaru da ke karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta lashe matsayi na uku na gasar a ranar Asabar.
’Yan wasan Indomitable Lions sun lallasa takwarorinsu na Burkina Faso da ci 5-3 a bugun fenareti bayan da aka tashi da ci 3-3.
- Abubuwan da ka iya kawo cikas ga Osinbajo a Zaben 2023
- AFCON 2021: Karon battar abokai tsakanin Salah da Mane a wasan karshe
Wani abin mamaki a wasan shi ne Burkina Faso ce ta fara zura kwallaye uku a ragar Kamaru cikin mintina 49 amma a karshe reshe ya juye da mujiya.
Kamaru ta yi kukan kura inda ta samu nasarar farke duk kwallaye ukun, lamarin da ya kai wasan ga bugun fenareti bayan da aka tashi da ci 3-3.
Kamaru dai ta kare a wasan neman matsayi na uku ne bayan da ta sha kaye a hannun Masar bayan bugun fenareti.
Hakan ya ba Masar din damar zuwa wasan karshe tare da Senegal.
Ita kuma Senegal ta kai wasan karshe ne bayan da ta doke ’yan wasan Burkina Faso da ci 3-1.